#EndSARS: Yadda zargin kisan da sojoji su ka yi wa masu zanga-zanga a Lagos ya harzuka jama’a

0

An yi zargin cewa masu zanga-zanga da dama sun mutu lokacin da Sojojin Najeriya su ka bude masu wuta a shingen biyan harajin masu ababen hawa (toll gate) da ke Lekki, Lagos.

Wannan kashe-kashe kan masu zanga-zanga wadanda ba su dauke da makamai ya faru ne sa’o’i kadan bayan Gwamnatin Jihar Lagos ta kakaba dokar-ta-baci.

Akalla wasu rahotanni sun ce mutum bakwai su ka mutu. Sai dai wasu jaridu sun ce adadin ya wuce mutum bakwai. Da yawan masu zanga-zangar sun samu munanan raunuka daga harbin bindigar da aka yi masu.

PREMIUM TIMES ta tabbatar cewa an rika kula da wadanda aka ji wa raunukan asibitoci daban-daban.

Da farko dai sojoji sun hana motocin agajin gaggawa karasawa har Lekki, domin su dauki wadanda aka jikkata zuwa asibitoci.

Jama’a Sun Harzuka

Wannan kisa ya janyo jama’a da dama a cikin Najeriya da sauran kasashen duniya sun harzuka.

Tsohuwar Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka, kuma wadda ta yi takarar shugabancin Amurka, Hilary Clinton, ta gargadi Shugaba Muhammadu Buhari “ya tsaida kisan masu zanga-zanga.”

Dama kuma tun a ranar Amurka ta rufe karamin ofishin jakadancin ta na da ke Lagos.

Fitaccen mawaki Davido ya nemi Buhari ya yi murabus. Haka Dan wasan Manchester United, kuma wanda ya buga wa Najeriya kwallo, Igalo, ya yi tir da Buhari a cikin filin wasan Kungiyar PSG ta Faransa, bayan kammala wasan su na farko na Gasar Champions League.

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki, shi ma ya yi tir da kisan.

Cikin kasashe da dama kuma ana ci gaba da yin tir da Gwamnatin Najeriya da kuma Shugaba Buhari, inda ‘yan Najeriya mazauna kasashen ke taron zanga-zangar nuna damuwa kan abin da ke faruwa a Najeriya.

A ranar Talata Majalisar Dattawa ta nemi Shugaba Buhari ya gaggauta yi wa ‘yan Najeriya jawabi. Amma dai har zuwa safiyar Laraba shiru ka ke ji.

Share.

game da Author