Kwanaki uku bayan tserewar daurarru 1993 daga kurkukun Benin a Jihar Edo, sojoji da jami’an tsaron kurkuku sun bude wa wasu daurarru wuta, a yunkurin tserewar da su ka yi daga kurkukun Ikeja da ke Lagos.
Wani da ke tsare a gidan kurkukun da bai yi yunkurin tserewa ba ne ya turo wa PREMIUM TIMES bidiyon yadda daurarrun su ka yi yunkurin guduwa da kuma yadda aka bude masu wuta.
Wannan yunkurin tserewa ya faru ne kwanaki uku bayan da wasu daurarru 1993 su ka tsere daga kurkukun Benin, a jihar Edo.
Majiyar ta cikin kurkukun, ta ce an harbi daurarru da dama a kokarin da su ka yi na balle kofar kurkukun na Ikoyi.
Majiyar PREMIUM TIMES ta ce an Yi rincimi sosai, har sai da ta kai an kira sojoji sun taya jami’an kurkuku dakile boren kokarin tserewar da daurarrun su ka yi.
PREMIUM TIMES ta kira Kakakin Yada Labarai na Hukumar Gidajen Kurkuku ta Kasa, Austin Njoku. An yi rashin sa’a wani ya dauki wayar, ya ce Njoku na cikin taron gaggawa. Amma ya ce zai sanar da shi idan ya fito.
Tun a ranar Litinin PREMIUM TIMES HAUSA ta ruwaito cewa an kafa dokar-ta-baci a Edo, bayan masu zanga-zanga sun fara kirkuku sun saki fursunoni.
Zanga-zangar #EndSARS ta koma tarzoma a Jihar Edo, yayin da masu zanga-zanga su ka fasa gidan kuskuku su ka saki fursunoni a Babban Kurkukun Benin.
Wannan ya tilasta wa Gwamna Godwin Obaseki na Edo kafa dokar-ta-baci tsawon awa 24, domin kokarin shawo kan lamarin.
PREMIUM TIMES ta gano cewa matasa ne su ka karbe ragamar zanga-zangar su ka kutsa su ka saki wasu daurarrun cikin kurkukun.
Matasan wadanda sun kai 100, wasun su day yawa sun samu raunuka ya yin da su ka yi arangama da artabu tsakanin su day jami’an tsaron kurkukun, wadanda aka ce sun rika harba bindigogi.
An Lalata Babbar Kotu
Baya ga fasa gidan kurkuku, an shiga Babbar Kotun Edo ta 4, aka lalata wani sashe na ta, sannan kuma aka yi awon-gaba da wasu ababen da ke cikin kotun.
Dama tun misalin karfe 7 na safe hasalallun su ka yi dafifi a kan Titin Sapele, su ka rika cinna wa tayoyi wuta, tare da maida masu motoci komawa baya.
Sun afka wa kurkukun yayin da su ka kara yawa sosai. Sun fasa wani sashe na dogon bangon kurkukun, inda wasu kuma su ka yi kumumuwar-shahadar-kuda, su ka taka bango da waya, su ka dira cikin kurkukun.
Wasu daurarrun sun gudu da harbin bindiga a jikin su, yayin da wani dattijo da ya fito aka kama shi, lokacin da aka farga ya na tafiya tamkar wanda ke bi ya na wucewa a gefen hanya.
Dokar Ta-baci: Gwamnatin Edo ta kafa dokar hana zirga-zirga tsawon awa 24, inda aka bada umarnin cewa daga karfe 4 na yamma ba a son ganin kowa a waje.
“Wannan doka ta zama tilas. Yayin da Gwamnatin Jihar Edo ke mutunta ‘yancan yin zanga-zangar lumana, to kuma ba za ta zuba ido wasu bayagari su tashi hankalin jama’a ba.
“Makarantu da wuraren hada-hadar kasuwanci su kasance a kulle, har zuwa lokcin da za a ji wani karin bayani daga bakin gwamnati.”