Rundunar ‘Yan sandan Najeriya ta tura jami’an kwantar da tarzoma a wasu sassan fadin kasar nan.
Hakan ya biyo bayan wani takarda da kakakin rundunar ‘yan sandan najeriya frank Mba ya saka wa hannu ne ranar Talata inda ya ce an yi haka ne domin samar da tsaro ga mutanen gasa, ganin yadda zanga-zangar #EndSARS ya dauki wani sabon Salo.
” An umarci kwamishinonin ‘yan sandan jihohin kasar nan da su sa ido wajen tsamo batagari cikin masu zanga-zanga domin hukunta su. Sannan kuma ana kira ga iyaye da su sa wa ‘ya’yan su ido da kwaban su game da kiyaye bin doka da oda.
Masu zanga-zanga sun dage cewa baza su hakura ba duk da shugaban Kasa MuhammadU Buhari ya amince da aiwatar da duka bukatunsu.
Ana ci gaba da batakashi tsakanin ‘yan sanda da masu zanga-zanga a wasu jihohi da suka hada da Ogun, Ondo, Legas Edo da babban birnin tarayy, Abuja.
A jihar Ogun, gwamnatin jihar ta sanar da rufe makarantu sannan ta hana Acaba a fadin jihar.
#EndSARS: ‘Yan iska sun yi wa mata uku masu zanga-zanga fyade a Ekiti -Cewar ‘Yan Sanda
Rundunar ‘Yan Sanda a Jihar Ekiti ta bayyana cewa wasu batagari sun kwace ragamar zanga-zangar #EndSARS, su ka rika amfani da damar su na aikata ayyukan assha.
Kakakin Yada Labarai na Rundunar ‘Yan Sandan Ekiti, Sunday Abutu, ya bayyana cewa wasu lalatatrun matasa sun rika yi wa mata masu zanga-zanga fyade a tsakar dare lokacin zanga-zanga a Ado Ekiti.
Ya ce mummunan lamarin ya faru a Dandalin Fajuyi Park, inda masu zanga-zangar su ka yi dandazo.
An kuma banka wa motoci uku wuta yayin zanga-zangar.
Wannan labari ne ya razana gwamnati har ta gaugauta sanarwar rufe dukkan makarantun Jihar gaba daya, na gwamnati na masu zaman kan su.
Gwamna Kayode Fayemi ya sanar cewa rufe makarantun ya zama tilas domin a tabbatar an tsare rayukan daliban jihar.
Run ranar Lahadi wajen karfe 8 na dare masu zanga-zanga su ka yi cincirindo a wasu muhimman wurare da ke babbban birnin jihar, musamman Dandalin Fajuyi Park.
Kwamishinan Shari’a na Ekiti, Okawake Fapohunda, ya yi da wannan fyade, wanda ya ce wasu batagari da ke cikin masu zanga-zanga ne su ka aikata.
“Saboda fyade da fashi da makami ba su cikin dabi’ar masu zanga-zangar #EndSARS.
“Yanzu ya zama wajibi a gaugauta fahimtar da masu zanga-zanga cewa akwai batagari a cikin su. Musamman ya kamata a sanar da mata su yi taka-tsantsan.”
Gwamna Fayemi ya ce an kulle makarantun kuma sai ranar 26 Ga Oktoba za a bude.
Discussion about this post