Ministan Tsaro Bashir Magashi, ya gargadi masu zanga-zangar #EndSARS kada su kuskura su keta hijabin da za su haifar da barazanar tsaro a kasar nan.
Magashi ya yi wannan barazana ce a lokacin da shi Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo da Sufeto Janar Muhammad Adamu ke bai wa masu zanga-zanga da sauran ‘yan Najeriya hakuri.
Minista Magashi ya yi gargadi ne a lokacin da Shugaban Kungiyar Kamfen din Buhari (BCO), Danladi Pasali ya kai masa ziyara, ranar Lahadi a Abuja.
Kakakin Ministan Tsaro, Muhammad Abdulkadir ne ya bayyana ganawar ta su da kuma abin da su ka tattauna, a cikin wata sanarwar da ya fitar.
Magashi ya nemi masu zanga-zanga cewa duk mai korafi ya koma karamar hukumar sa ko jihar sa ya mika kukan sa.
Gargadin da sojoji su ka yi na ranar Asabar ya harzuka masu zanga-zanga a shafukan zumunta na soshiyal midiya. Sai kuma wata magana da Ministan Yada Labarai ya yi, inda ya ce, ba za su bari masu tada zaune tsaye su harzitsa Najeriya ba.
Wannan bayani ya zo ne kwana daya bayan Gwamnatin Tarayya ta ce ba za ta bar masu tada tarzoma su yamutsa Najeriya ba.
Gwamnatin Tarayya ba za ta zuba ido masu tayar da tarzoma su hargitsa Najeriya, ta hanyar daukar doka a hannun su ba.
Wannan kalami ya firo ne daga bakin Ministan Yada Labarai Lai Mohammed, lokacin da aka yi wata doguwar tattaunawa da shi, ranar Asabar da dare, a Gidan Talbijin na NTA.
Ya yi kakkausan gargadin, ganin yadda zanga-zangar lumanar da ake yi domin rashin amincewa da Jami’an SARS, ta barke zuwa fito-na-firo da arangama a wasu wurare.
Furucin Lai ya zo ne kwana biyu bayan da Rundunar Sojojin Najeriya ta sanar cewa ba za ta zuba ido wasu tsiraru su dauki doka a hannun su ba.
Sojojin Najeriya sun ce ba za su bari wasu su gurgunta dimokradiyyar kasar nan ba. Kuma sun kara jaddada goyon bayan su da biyayya ga Shugaba Buhari.
Ya ce harin da aka kai wa Gwamna Oyetola na Osun ya nuna cewa ‘yan-ta-more sun kwace ragamar jagorancin zanga-zangar lumanar da ke gunada sama da mako daya.
Ya ce zai iya yiwuwa wadanda su ka tsara zanga-zangar nan da kyakkyawar manufa su ka shirya ta. “Amma dai tabbas abubuwan da ke faruwa sun nuna cewa lallai marasa kishi da ‘yan daba sun kwace ragamar zanga-zangar.
” Yanzu fa ba masu zanga-zangar #EndSARS gwamnati ke fuskanta ba. Kawai wasu dandazon ‘yan a-fasa kowa ya rasa sun karbe ragamar zanga-zangar.
“Don haka tilas gwamnati ta tashi tsaye domin kada abin ya kai ga jefa kasar nan cikin mummunan hargitsi.
“Wajibin Gwamnatin Tarayya ne ta tashi tsaye domin ta kare rayuka, dukiyoyi da lafiyar ‘yan Najeriya.
Ya yi nuni da yadda aka fara samun rahotanni da su ka tabbatar da asarar rayuka a wurin zanga-zanga. Sai tare hanyoyi da ake yi masu tafiya wuraren aiki ba su samun damar zuwa aiki.
Har ila yau, Minista Lai ya ce gwamnati na ganin zanga-zangar wata kullalliya da manufa ce boyayya ta neman dagula gwamnatin Buhari da kuma dagula Najeriya baki daya.
Ya ce tunda gwamnatin Buhari ta amince ta biya dukkan bukatun masu zanga-zangar, bai ga dalilin ci gaba da zanga-zangar ba.
Lai ya roki ‘yan Najeriya hi su kalli zanga-zangar da idon basira, za su game da akwai wata boyayyar manufar dagula wannan gwamnati da Najeriya baki daya.