#EndSARS: Masu zanga-zanga sun kashe DCO bayan sun banka wa ofishin ƴan sanda wuta

0

Wasu ƴan iskan masu zanga-zanga sun kai wa ofishin DCO na Ado-Odo da ke Jihar Ogun hari, su ka banka masa tare da kashe DCP Augustine Ogbeche.

Kakakin Yaɗa Labarai na ‘Yan Sandan Jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi ya tabbatar da wannan aika-aika, ya nuna bakin cikin yadda wasu ƴan iskan gari su ka karbe ragamar zanga-zangar lumana, su ka maida abin tarzomar daukar doka a hannun su.

“Da safiyar Laraba masu zanga-zanga sun je ofishin ‘yan sanda na Atan-Ota su ka banka masa wuta. Kuma su ka kashe DCP Augustine Ogbeche. Wani farar hula kuma ya mutu a wurin, sannan kuma sun kwashi makamai sun gudu da su.

Ya kara da cewa kuma an ji wa DOP Sikiru Olugbenga rauni, sannan har zuwa lokacin da aka fitar da wannan sanarwa ga manema labarai, ba a san inda DOP din ya ke ba, ko halin da ya ke ciki.

A kan haka, ya ce Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Ogun ya roki matasa su yi hakuri a zauna lafiya, su guji tayar da hankula.

PREMIUM TIMES HAUSA ta buga wasu labaran yadda masu zanga-zanga su ka ragargaza Fadar Oba na Lagos da gidan mahaifiyar Gwamnan Lagos bayan sun kone wani ofishin ‘yan sanda.

Duk da dokar-ta-baci da aka kafa a Lagos, mafusatan masu zanga-zanga sun fito sun ci gaba da kona muhimman wurare a cikin Lagos.

A safiyar Laraba an ragargaza Fadar Oba na Lagos, Eilwanu Akiolu, kuma aka rika jidar kayayyaki masu muhimmanci da tsada ana guduwa da su.

Wani bidiyo da aka nuna, an ga matasa na gudu bayan sun fito daga fadar, kowa ya rungumo kayan sata. An ga wani a gaba dauke da sandar mulkin Babban Basaraken na Lagos.

Hadimin Sarki Rilwani ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa an kutsa cikin fadar an saci kaya masu yawa. Kuma an ragargaza wasu sassa na cikin fadar. Deoye Olumegbon, wanda shi ma Dan sarauta ne, ya ce an yi babbar barna a fadar.

Yadda Sojoji Su Ka Ceci Sarkin Lagos Daga Hannun Masu Zanga-zanga

Hadimin sa ya ce yayin da masu zanga-zangar su ka gama ragargaza ofishin ‘yan sanda na Ebute Ero, sai su ka yi wa Fadar Oba na Lagos tsinke. Ganin yadda aka kewaye gidan ana kwasar kaya, sai aka kira sojoji domin su kai masa dauki.

“Nan take aka turo sojoji cike da motoci biyar, su ka kutsa su ka ceto shi.”

Eilwanu Akiolu dai tsohon babban jami’in dan sanda ne, kuma dan jam’iyyar APC ne rikakke.

A zaben 2015 ya yi barazanar korar baki daga Lagos, wadanda ba ‘yan asalin jihar ba, matsawar ba su zabi Akinwunmi Ambode da Buhari a lokacin zabe ba.

An Lalata Gidan Mahaifiyar Gwamnan Lagos, Sanwo-Olu

Wani rahoto kuma ya tabbatar da cewa masu zanga-zanga sun ragargaza gidan mahaifiyar Gwamnan Lagos da ke unguwar Surulere, kan titin Akerele Street, a Lagos.

Wani jami’i ya tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa an ragargaza gidan sai dai bai san ko da me da me aka sace ba.

Zanga-zangar ta yi muni bayan kashe masu zanga-zanga da sojoji su ka yi a Lekki da tsakar daren Talata.

Share.

game da Author