#EndSARS: Majalisar Dinkin Duniya ta yi magana kan zargin kisan masu zanga-zanga a Lekki, Lagos

0

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antoio Guterres, ya yi tir da kisan da aka zargi sojoji su ka yi wa masu zanga-zanga a Lekki da ke Lagos a ranar Talata.

A cikin jawabin sa da Kakakin Yada Labaran sa, Stephane Dujarric ta sa wa hannu, Guterrres ya ce abin da ke faruwa a Najeriya abin tir da assha ne matuka.

An wallafa wannan bayani a cikin shafin labarai da bayanan UN na intanet a safiyar Laraba.

Daga nan kuma ya yi kira da a gaggauta kawo karshen cin zarafin da ‘yan sanda ke wa jama’a a Najeriya.

“Ya yi tir da yadda aka yi sakacin bari har zanga-zanga ta yi munin da ya haifar da kisa a ranar 20 Ga Oktoba. Sannan kuma ya na yi wa iyalan wadanda aka rasa din ta’aziyya da jaje da jimami. Ya yi kira ga mahukuntan Najeriya su lalubo matakan shawo kan rikicin maimakon yin amfani da karfin soja.

Ya jaddada aniyar Majalisar Dinkin Duniya wajen taimakawa a samu mafitar magance matsalolin.

Kafin Majalisar Dimkin Duniya ta yi magana, dan takarar Amurka Biden ya roki Amurka ta tsaya bayan masu zanga-zanga.

Tsohon Mataimakin Shugaban Amurka Joe Biden kuma dan takarar shugaban kasa a zaben Amurka da ake kai, a karkashin jam’iyyar Democrat, ya bayyana cewa ya zama tilas Amurka ta goyi bayan masu zanga-zangar #EndSARS a Najeriya.

“Wajibin Amurka ne ta goyi bayan masu zanga-zangar neman sauya fasalin jami’an ‘yan sandan Najeriya da kuma kawo karshen cin hanci da rashawa a kasar.”

Biden ya fitar da wannan sanarwa a ranar Talata da dare, Jim kadan bayan an bude wa masu zanga-zanga wuta a Lekki, Lagos.

Biden ya ja hankalin gwamnatin Najeriya cewa cewa ta nemi zama kan teburin shawarwari da kungiyoyin kare dimokradiyya da na kare hakkin jama’a.

“Wannan zai kawo karshen korafe-korafe da fushin da ake yi dangane da rashin adalci. Kuma zai sa kowane mai korafi ya ji cewa an jawo shi wajen gina ingantacciyar Najeriya.”

“Ina kira ga Shugaba Buhari da sojojin Najeriya su su dakatar da tarzomar zubar da jini kuma su daina bude wa masu zanga-zanga wuta a Najeriya, ganin tuni har zanga-zangar ta ci rayuka da dama.” Cewar Biden.

A jiya Talata din ce dai da dare, tsohuwar Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka, Hillary Clinton ta gargadi Najeriya ta daina bude wa masu zanga-zanga wuta.

Hillary wadda ta yi takarar shugabancin Amurka karkashin Democrats a zaben 2016, ta ce ba daidai ba ne a bude wa masu zanga-zangar lumana wuta.

Share.

game da Author