Sanata Kabiru Marafa, ya ja hankalin Shugaba Muhammadu Buhari ya buɗe idanun sa garau, ya kalli yadda ake gudanar da zanga-zangar da ya ce da Buhari ake, ba wai kai-tsaye da ƴan sandan SARS ake ba.
Marafa wanda ya nemi tsayawa takarar gwamnan Zamfara a karkashin APC, a zaɓen 2019, ya ce idan ba a yi hankali ba, rushe SARS da Buhari ya yi, zai iya haifar da manyan matsaloli masu yawa a ƙasar nan.
Ya ce tunda babu jihohin Arewa a jerin inda ake zanga-zanga kan SARS, to Buhari ya farga cewa wani tuggu ne aka kitsa wa gwamnatin sa, musamman saboda zaɓen 2023, amma ba takamaimen zanga-zangar SARS ba ce.
Ya ce mutanen sun gina wa Buhari rijiya, kuma har ya zurma kafar sa ɗaya, ta hanyar rusa Rundunar SARS da ya sa aka yi.
“Idan na yi la’akari da inda na fito. Ba ka da yadda za a yi na goyi bayan rusa SARS. Ka na nan wata rana kuma mutane za su fito su na zanga-zanga cewa gwamnati ta kasa kare rayukan su.
“Za a shiga kauyen da ke da mutum 3000, cikin awa biyu a kashe mutum 200. Duk mutane ba su yi wannan zanga-zangar ba. Sai don wasu tsirarun jami’an tsaron SARS sun aikata ba daidai ba, a yi zanga-zangar rusa Rundunar SARS mai kula da tsaro sukutum.
“Shin a irin yadda mu ke fama da matsalar tsaro a kasar nan, za mu iya zama ba tare da SARS a yadda su ke a yanzu ko a cikin wata canjin siffa ba? Ba zai yiwu ba.” Cewar Marafa.
Ana dai ci gaba da zanga-zanga ne duk da cewa an rusa SARS. Masu zanga-zanga na neman a ruguza rundunar kwata-kwata.
Ana zargin SARS da kama mutane ba tare da dalili ba, tsare wanda bai ji ba kuma bai gani ba, tatsar makudan kudade daga masu laifi da wadanda su ke yi wa sharri.
Sannan kuma ana yawan samun rahoton kashe mutane ba gaira ba dalili da jami’an SARS ke yi.
Masu zanga-zanga na ci gaba da neman a gurfanar da ‘jami’an SARS da aka zarga da aikata laifukan take hakkin dan Adam.
Zanga-zanga ta ci gaba da muni, musamman saboda rahotannin kashe masu zanga-zanga a wasu jihohi.
Kungiyar Kare Hakkin Jama’a ta Amnesty International, ta ce an kashe mutum goma a garuruwa daban-daban na Najeriya.