#EndSARS: Kashi 6 cikin kashi 10 na ƴan Najeriya sun goyi bayan zanga-zangar da aka gudanar

0

Wani bincike da aka gudanar cikin Oktoba din nan, ya nuna cewa kashi 6 cikin kashi 10 na ƴan Najeriya sun goyi bayan zanga-zangar #EndSARS da aka yi.

A cikin mutum 1,114 da aka ji ra’ayin su, wadanda sun kumshi maza kashi 51, mata kuma kashi 49, ta ji ra’ayoyin masu shekaru 18 zuwa sama a duniya.”

Binciken ya nuna kashi 61 bisa 100 na wadanda su ka amfa tambayoyi, sun goyi bayan zanga-zangar lumanar da aka yi, domin nuna wa gwamnatin tarayya fushi, akan yadda jami’an SARS ke cin zarafin wadanda bas u jib a, bas u gani ba.

Abin mamaki kuma an samu har kashi 4 cikin 100, wadanda su ka ce su ba su ma san abin da ake ciki ba. wato ba su san ana zanga-zanga a kasar nan a lokacin ba.

Kashi 35 bisa 100 na wadanda aka tuntuba din kuma sun ce bas u goyi bayan fita yin zanga-zangar ba.

“Wannan bincike ya kara nuna cewa masu zurfin ilmi ne suka fi goyon bayan zanga-zangar, domin kashi 70 na wadanda aka su ka nuna goyon baya, duk sun kammala jami’a, ko kuma sun kammafa makarantun gaba da sakandare. Kashi 15 kadai a cikin su wadanda bas u da ilmi a wadanda aka ji ta bakin na su.

“Haka kuma binckien ya nuna kashi 91 bisa 100 na ‘yan kudancin Najeriya sun goyi bayan zanga-zangar. A Arewa kuwa kashi 35 bisa 100 ne kacal su ka goyi baya.

Dattawa masu shekaru 60 zuwa sama kuwa, kashi 70 bisa 100 na su sun goyi baya. Yayin da masu shekaru 36 zuwa 60, kashi 65 din su ne su ka goyi baya.

Masu shekaru 18 zuwa 35 a duniya kuwa, an samu kashi 53 na su da suka goyi baya.

“Bincike ya nuna cewa duk da zanga-zangar #EndSARS duk matasa ne su ka kirkiro ta kuma su ka assasa ta, to dattawa ma sun fara fitowa kenan sun a nuna rashin jin dadin rashin adalcin da su ka yi korafin ana yi a kasar nan, har ma sun a kiraye-kirayen a saisaita Najeriya daga karkacewar da ta yi.

“Kashi 43 cikin 100 sun nuna rashin amincewa da tafiyar gwamnatin Shugaba muhammadu Buhari. Kashi 28 kuma korafin su a kan rashin aikin yi ne. sai wasu kashi 27 da su ka nuna takaicin yadda lyan sanda ke cin zarafin jama’a. Masu neman a sauya fasalin tafiyar gwamnati sunkai kashi 60 bisa 100.

Wasu kuma takaicin su shi ne yawan zaman gida da daliban jami’a key i saboda yawan yajin aikin malaman jami’a a karakashin mulkin Buhari.

Wasu da dama kuma sun rika bada labarin irin gallazawa da gwagwarmayar da su ka sha fuskanta ko su ka taba fuskanta a lokacin da su ka fada hannun ‘yan sanda.

Share.

game da Author