Wani jigo a jam’iyyar APC, Ibrahim Mohammed, ya roki shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya gaggauta karkatar da hada-hadar jiragen ruwa daga Legas zuwa jihar Ribas saboda abubuwan dake faruwa.
” Kowa dai ya ga yadda ‘yan iska a Legas suka rika banka wa ofishohin gwamnati wuta har da ofishin hukumar kula da tashohin ruwan Najeriya dake Legas sannan sun hana a ci gaba da ayyuka kamar yadda aka saba.
” Dama kuma akwai manyan tashohin ruwa jihar Ribas dake aiki yanzu haka, kawai a bunkasa su sannan a fadada na Baro dake jihar Neja sda sauran su, domin a cigaba da aiki maimakon a cigaba da amfani da na Legas.
A wasikar, Ibrahim yace yanzu abin ya kazanta, domin ‘yan iska sun na neman karfi da yaji a samu rarrabuwar kai da tashin hankali. Abin ya kazanta saboda haka dole gwamnati ta karkata akalar zuwa wani gefen tunda wuri.
Idan ba a manta ba tun bayan fara #Zanga-Zangar #EndSARS, tsaro ya tabarbare a wasu jihohin kasar nan. Har zuwa safiyar Asabar din yau, ‘yan iska na ci gaba da bankawa gidajen gwamnati wuta da kuma sace sace a jihohin Legas, Oyo, Osun, Ekiti Koros Ribas da sauran su.
A jihar Kwara ma an yi bata kashi tsakanin jami’an hukumar Kwastam da ‘yan iska da suka dira musu. Wasu jami’ai sun samu rauni a bata kashin.