Tsohuwar Sakatariyar Kasa, ta kasar Amurka, Hillary Clinton ta gargadi Buhari da ya daina Kashe mutanen kasar sa ta hanyar saka sojoji suna harbin su a wajen zanga-zanga.
Clinton ta rubuta a shafinta ta tiwita cewa ” Ina kira ga Buhari da rundunar Sojin Najeriya da su daina kashe matasa masu zanga-zangar #EndSARS a Najeriya.
Tsohon dan kwallon Najeriya da buga kwallo a kasar Birtaniya ya gargadi ‘yan Najeriya da su zauna a gidajen su domin tsare rayukan su daga fushin sojojin Najeriya wanda aka basu damar su kashe masu zanga-zanga.
Ighalo wanda ke buga Kwallon a kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ya bayyana cewa shi ba mai magana bane, amma abinda aka yi wa mutane a Legas ranar Talata yasa dole ya fito yayi magana.
” Abinda aka yi wa masu zanga-zangar #EndSARS ya wuce misali, ina kira ga gwamnatocin duniya da majalisar Dinkin Duniya su sa baki akan abinda ke faruwa a Najeriya. Wannan gwamnatin kashe mutane ne.
” Sojoji sun bude wa masu zanga-zanga da basu ji ba basu gani ba wuta, inda suka kashe mutum 7 sannan da dama sun samu rauni. Wannan abu bai yi dadi ba. Amma kuma wannan gwamnati dama gwamnati ce da bata damu da mutanenta ba da kuma yadda ake gudanar da mulki a kasar.
A daren Talata an samu rahoton yadda sojojin Najeriya suka bude wa masu zanga-zanga wuta a Legas. A bayanan da suka fito bayan wannan arangama sun nuna cewa akwai mutum bakwai da suka rasa rayukan su sannan wasu da dama sun samu raunuka a jikin su.
Discussion about this post