#EndSARS: Gaggan masu kutse sun kwace shafin Twitter na Hukumar Gidajen Radiyo da Talbijin ta Najeriya

0

Kwana ɗaya bayan sun kwace shafin intanet na Rundunar Ƴan Sandan Najeriya (NPF), yanzu kuma gaggan ƙadangarun bariki na duniya masu shigar-kutsen shafukan intanet, sun kwace shafin Twitter mallakar Hukumar Kula da Gidajen Radiyo da Talbijin ta Najeriya (NBC).

Wadannan gungun mashahuran-boye, kuma gaggan ƙadangarun barikin tashoshin intanet na duniya, sun yi sanarwa a ranar Juma’a cewa sun ci gaba da nuna goyon bayan zanga-zangar #EndSARS, ta hanyar kwace shafin Twitter na Hukumar NBC.

Sun fitar da sanarwa kamar haka:

“Yekuwa jama’a. Mu ne dai kadangarun barikin nan da ba mai iya gano mu ko su wa ne.

“Mun karya shafin intanet na Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya. Mun kwace shafin Twitter din Hukumar NBC.

“To shafin wace hukumar gwamnati kuma ku ke so mu kutsa mu durkusar da ita?”

Ta Baya Ta Raggo: Daga baya kamfanin sarrafa fasahar zamani ta shafukan intanet, Glaxy Backbone, ta shigo da wani siddabatun da ta sanar cewa duk wata hukuma, ko cibiya ko ma’aikatar gwamnati za su yi amfani da su a matsayin garkamemen makullin kulle shafukan su, domin hana masu kutse kwacewa.

PREMIUM TIMES a ranar Alhamis ta bada labarin yadda Gaggan ‘yan buruntu sun kutsa cikin rumbun bayanan sirrin ‘Yan Najeriya na intanet.

An kasa shiga rumbun tattara bayanan Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya bayan da wasu gaggan kadangarun bariki masu shigar-kutse a shafukan intanet din hukumomin gwamnati sun kwace shafin.

Dama kuma wadannan masu shigar-kutse da su ka yi kaurin suna a duniya, sun bayyana karara cewa za su kutsa cikin shafukan intanet din hukumomin gwamnati, domin nuna goyon bayan su ga zanga-zangar #EndSARS, ‘yan sandan da sunan su ya baci wajen gallaza wa wadanda ba su ji ba, ba su kuma gani ba.

Wadannan gungun masu shigar-kutse a shafukan intanet, wato “hacktivists” wato ‘yan-a-kutsa, babu wanda zai ce ga ko su wane ne, saboda komai a asirce su ke yi.

Sai ma da su ka yi sanarwa a shafin su na Twitter cewa za su kutsa cikin shafukan hukumomin gwamnati. Kuma su na da mabiya a Twitter sama da mutum milyan biyar.

Kafin su kutsa cikin shafin bayanan Rundunar ‘Yan Sanda, sai da su ka yi sanarwar nuna goyon bayan zanga-zangar neman a rushe SARS.

Bayan ta kutsa kuma sai su ka saki sunayen da bayanan jami’an ‘yan sanda, adireshin su da lambobin asusun ajiyar su a bankuna.

Duk kokarin shiga shafin intanet din ya gagara, saboda ‘yan kutse sun kwace shi.

Kafin buga labarin an kasa samun kakakin yada labarai na ‘yan sanda domin karin bayani.

Sun taba yin irin wadannan kutse a Amurka, Israila, Tunisiya, Uganda da wasu kasashe.

Share.

game da Author