An kasa shiga rumbun tattara bayanan Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya bayan da wasu gaggan kadangarun bariki masu shigar-kutse a shafukan intanet din hukumomin gwamnati sun kwace shafin.
Dama kuma wadannan masu shigar-kutse da su ka yi kaurin suna a duniya, sun bayyana karara cewa za su kutsa cikin shafukan intanet din hukumomin gwamnati, domin nuna goyon bayan su ga zanga-zangar #EndSARS, ‘yan sandan da sunan su ya baci wajen gallaza wa wadanda ba su ji ba, ba su kuma gani ba.
Wadannan gungun masu shigar-kutse a shafukan intanet, wato “hacktivists” wato ‘yan-a-kutsa, babu wanda zai ce ga ko su wane ne, saboda komai a asirce su ke yi.
Sai ma da su ka yi sanarwa a shafin su na Twitter cewa za su kutsa cikin shafukan hukumomin gwamnati. Kuma su na da mabiya a Twitter sama da mutum milyan biyar.
#Nigeria: Anonymous hacks multiple government websites in solidarity with #EndSARS protestors and retribution for violence by police. #OpNigeria #EndSARSProtest
src: https://t.co/cjDdEfPB8w pic.twitter.com/F2J7qvz35W
— Anonymous (@YourAnonCentral) October 14, 2020
Kafin su kutsa cikin shafin bayanan Rundunar ‘Yan Sanda, sai da su ka yi sanarwar nuna goyon bayan zanga-zangar neman a rushe SARS.
Bayan ta kutsa kuma sai su ka saki sunayen da bayanan jami’an ‘yan sanda, adireshin su da lambobin asusun ajiyar su a bankuna.
Duk kokarin shiga shafin intanet din ya gagara, saboda ‘yan kutse sun kwace shi.
Kafin buga labarin an kasa samun kakakin yada labarai na ‘yan sanda domin karin bayani.
Sun taba yin irin wadannan kutse a Amurka, Israila, Tunisiya, Uganda da wasu kasashe.
Discussion about this post