Shugaba Muhammadu Buhari ya roki a zauna lafiya, hakuri da kuma kai zuciya nesa. Kiran ya zo ne kwana daya bayan zargin sojoji sun bude wa masu zanga-zanga wuta, sun kashe wasu a Lekki, cikin Lagos.
Gwamna Babajide Sanwo-Olu na Lagos, ya ce wadanda su ka yi kisan wasu ne da sun fi karfin tsawatarwar gwamnatin sa.
Ya ce gwamnatin jihar sa ba ta da iznin sa sojoji su yi ko su bari. Ya dora laifin a kan gwamnatin tarayya.
Sojoji a karkashin shugaban kasa su ke, kuma shi ne Babban Kwamandan Askarawan Najeriya. Wato kenan babu mai iya bada iznin a bude wuta sai Shugaba Buhari.
Cikin wata sanarwa da kakakin sa Femi Adesina ya sa wa hannu, Buhari ya roki a yi hakuri, a kai zuciya nesa, sannan kuma a guji tarzoma.
Sai dai har a karshen bayanin babu inda ya yi maganar kisan da sojoji su ka yi a Lekki.
Daga nan ya jaddada aiwatar da canje-canje a hukumar ‘yan sanda da kuma aiwatar da dukkan kudirorin da Kwamitin Shugaban Kasa kan SARS ya ce a zartas.
Ana ta kiraye-kirayen Buhari ya fito ya yi wa ‘yan Najeriya jawabi dangane da halin da ake ciki.
Zanga-zangar da aka fara kwanaki biyu domin neman a rushe SARS, tuni ta rikide ta koma mummunar tarzoma, musamman a Lagos, inda ake ci gaba da kona kadarori da hukumomin gwamnatin tarayya da na jihar Lagos da kuma na jigon jam’iyyar APC, Bola Tinubu.