Shugaba Muhammadu Buhari ya shaida wa kasashen duniya da manyan kungiyoyin kasa da kasa cewa su guji gaggawar yanke hukunci dangane da labaran da ake watsawa kan tarzomar #EndSARS.
#EndSARS wani kamfe ne da matasan Najeriya su ka kirkiro kuma su ka assasa domin nuna damuwar su kan yadda ‘yan sandan Najeriya ke gallaza masu har abin kan kai ga kisan wanda bai ji ba, bai kuma gani ba.
Zanga-zangar ta ja hankalin kasshen duniya, ciki har da Amurka.
Zanga-zangar ta kara Jan hankalin duniya a ranar Talata da dare, sanadin bude wa masu zanga-zanga wuta a Lekki da ke Lagos da sojoji su ka yi.
An tabbatar da mutuwar mutum biyu da kuma ji wa wasu da dama raunuka a Lekki.
Cikin wadanda su ka yi tir da bude wutar har da tsohuwar Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka, Hillary Clinton.
A jawabin sa na ranar Alhamis, makonni biyu da barkewar zanga-zangar, Buhari ya ja hankalin kasshen duniya su daina gaggawa wajen yanke hukunci daga jin labarai wadanda kan kasance na kan teburan mai shayi ne.
Maimakon haka, Buhari ya ce su rika neman sanin hakikanin abin da ya faru daga gwamnatin sa tukunna, kafin su dauki wata matsaya.
Duk da hotuna da bidiyon abin da ya faru, hukumar sojojin Najeriya ta ce babu wani sojan ta da ya yi harbi a wurin.
Majalisar Dinkin Duniya ita ma ta yi tir da harbin da aka yi wa masu zanga-zangar.
Akalla an banka wa murare sa kadarorin gwamnati wuta kimanin 40 a jihohin kasar nan.
Ofisoshin ‘yan sanda da gidajen kurkuku da manyan hukumomin gwamnatin tarayya aka fi banka wa wuta.