EndSARS: ‘Buhari ka yi wa ‘yan Najeriya jawabi kafin wuri ya kure maka’ -Shawarar Sarkin Ibadan

0

Babban Basaraken Kasar Ibadan, Olubadan na Ibadan, Saliu Adetunji, ya gargadi Shugaba Muhammadu Buhari ya gaggauta yi wa ‘yan Najeriya jawabi.

Ya ce jinkirin da Buhari ke yi, zai iya sa duk wani abu da zai fada a gaba, zai kasance an makara ne.

Ya ce yin jawabi ga ‘yan Najeriya da Buhari ya kamata ya yi, zai iya yayyafa wa wutar rikicin da ya tirnike ruwan sanyi domin ta lafa.

Adetunji, ya bayyana halin da kasar nan ke ciki cewa matsananci ne kuma ya wuce gona-da-iri, ya ce duk da haka idan Buhari ya yi magana kafin wuri ya kure, zai iya yayyafa wa hargitsin wutar ruwa ta lafa.

“Mutanen mu sun shiga wani mawuyacin hali kuma mai tsananin gaske a cikin makonni biyun da su ka gabata.”

“Na yi amanna shugaban da al’umma su ka zaba da kan su, zai iya magana su saurare shi, har ya kawo karshen wannan zanga-zanga da ta dauki tsawon lokaci ana gudanar da ita.”

Basaraken ya yi wannan bayani ne cikin wata takardar da Kakakin Yada Labarai na sa, Adeola Okolo ya aiko wa PREMIUM TIMES.

“Duk wani wanda zai fito ya yi magana, idan ba shugaban kasa ba ne da kan sa, to kawai bata bakin sa zai yi.”

“A matsayin sa wanda ya yi rantsuwar kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya da tattalin arzikin kasar, ya zama wajibi gare shi ya yi wa al’ummar kasar nan jawabi.”

Olubadan ya nuna takaicin yadda ‘yan iska su ka kwace ragamar zanga-zangar #EndSARS, alhalin ba su ma san makasudin zanga-zangar ba.

Ya bada shawarar a gaggauta sasantawa da Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa domin a koma makaranta, matasa su shagaltu da nazari da daukar darasi.

Share.

game da Author