Maitaimaka wa gwamnan jihar Kano kan harkokin yada labarai, Salihu Tanko Yakasai ya ragargaji shugaban Kasa Muhammadu Buhari inda ya ce bashi da tasusayi da sanin ya kamata.
Tanko ya bayyana haka ne a nuna goyon bayan sa ga kira da ‘Yan Najeriya keyi na a rusa rundunar ‘yan sanda na SARS, yana mai yin suka da salon mulkin Buhari game da abubuwan da suka shafi talakawa.
A hira da yayi da PREMIUM TIMES ta wayar Salula, Tanko ya ce Buhari ya ba talakawa kunya wadanda sune suka yi ruwa sukayi tsaki ya dare kujerar mulkin Kasar nan.
” Ban taba ganin lalatacciyar gwamnati da babu ruwanta da halin da mutanenta ke ciki irin gwamnatin Buhari ba, a duk lokacin da mutanen sa ke cikin yanayin kunci da damuwa, maimakon ya bi su ya lallashe su, babu abinda ya dame shi da su.
” Rashin nuna halin-ko-in kula da ko ohon sa ga batutuwa irin haka, nashi na musamman ne.
” Ka fito ka kwantar wa jama’ar ka hankula na minti biyar ya zama maka aiki. Sai kaga kamar kana yi musu wani alfarma ne ba su cancanta a yi musu haka ba.
” Sannan kuma wadannan mutane sune wadanda ka zazzagaya jihohin 36 na kasara nan kana neman kuri’un su amma babu abinda ya dame ka da su yanzu.
#EndSARS: Jami’an Tsaro Ko Jami’an Aika-aika? Yan Najeriya sun ce basu so
An kafa SARS domin dakile manya ko muggan laifuka da su ka hada da fashi da makami da garkuwa da mutane da sauran mugayen mutanen da ke hana al’umma zaman lafiya.
Sannu a hankali sai wasun su aka rika amfani da su wajen gallazawa, azabtarwa ko kuma ‘koya wa wani ko wasu hankali’ ta hanyar da shari’ar tsarin dokar kasa bai tanadar ba.
Maimakon al’ummar da ake so a kare lafiya, rayuka da dukiyoyin su su rika murnar kafa SARS, sai yawancin mutane su ka koma yin da-na-sanin kafa SARS.
Jami’an SARS da dama su na kallon kan su tamkar sun fi dokar ita kan ta kan ta karfi. Duk wani korafi, kuka, karajin da ake yi na a rushe rundunar SARS, ba abin mamaki ba ne, domin yawancin masu arba da su, da wuya su wanye lafiya.
SARS ba su jin ko dar-dar wajen darzaza harbi dararam, ko da kuwa a kan harkar tankiya, gardama ko sabani ne.
A kullum a jaridu a na samun rahotannin wadanda SARS su ka kashe, ko su ka jikkata, ko su ka lahanta.
Cikin watan Satumba ‘yan Najeriya sun sake kokartawa wajen tashi haikan su na kiraye-kirayen a rushe SARS. Abin ya yi karfi har ta kai cikin Oktoba din nan an ta zanga-zanga a jihohi daban-daban na kasar nan
Ba a bar manya wajen korafi da irin abin da su ke kira “ta’asar da SARS ke yi” ba. Ranar Laraba tsohon Mataimakin Shugaban Kasa ya yi Allah wadai da yadda wasu jami’an tsaro na SARS ke gallaza wa talakawa da ma masu karfin baki daya.
SARS, rundunar da aka kafa don dakile fashi da makami da manyan laifuka, sun koma hatta matasa maza masu yin askin ‘yarbatsula’, wanda ake barin gashi a cukuikuye ko kitso, kamawa su ke yi.
Haka nan SARS kan damke matashin da su ka gani da rankwaleliyar waya. Kafin ta tabbatar masu cewa ba ta sata ba ce, tuni jikin ka ya yi tsami, ya kumbura, ka koma ta neman ran ka.
Azabtarwar da su ke wa jama’a ta kara harzuka ‘yan Najeriya har aka shiga zanga-zangar neman a ruguje rundunar.
Hatta ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje, sun shiga sahun masu neman a rushe SARS.
Ya rage ga a duba a ga shin amfannin su ko rashin amfanin su, wane ya fi rinjaye? Amma dai aikace-aikacen SARS abin dubawa ne. Saboda ko makaho ya yi arba da su, zai iya ce maka harkar ta su akwai aika-aika.
Wanda ya shiga hannun SARS da ganganci ko da tsautsayi ko azal, shi ne zai tabbatar da cewa kirarin da ake wa dan sanda wai abokin kowa, to tatsuniya ke kawai!