#EndSARS: An hana zanga-zanga a Abuja – Mahukunta

0

Ministan Abuja, Mohammed Bello ya sanar cewa daga yanzu jami’an tsaro ba za su sassauta wa duk wanda ya fito zanga-zanga a fadin babban birnin tarayya ba cewa an hana zanga-zanga a Abuja daga yau.

Kakakin minista Bello, Anthony Ogunleye, ya bayyana cewa masu zanga-zangan sun fara wuce gona da iri sannan kuma da kin bin dokokin Korona da ke aiki a fadin babbar birnin Tarayyar.

A dalilin haka, ministan ya ce kowa ya hakura haka nan ya koma gida.

Idan ba a manta ba gwamnatin tarayya ta amince da bi abinda masu zanga-zanaga suke so, sannan kuma ta rushe rundunar SARS din amma kuma matasan sun ki su jan ye a manyan titunan biranen kasar nan, musammam a Legas da Abuja da wasu jihohin kudancin Kasar nan.

A ranar Laraba, sai da wasu ‘yan daba suka fatattaki masu zanga-zanga a Abuja, haka kuma a jihar Legas suma, ranar Alhamis, masu zanga-zanga sun yi arangama da wasu hasalallun matasa da suka ce suma zanga-zangar ya ishe su hakan nan.

Share.

game da Author