#EndSARS: An babbake ofishin ‘Yan sanda a Legas

0

Hasalallun masu zanga-zangar #EndSARS sun cinnan wa ofishin ‘Yan sanda wuta a jihar Legas, bayan fatattakar yansanda da suka yi da ofishin su.

A wani bidiyo da aka rika yadawa a kafafen sada zumunta na yanar gizo, an nuna yadda ‘yan sanda suke tafka gudu dauke da jakukkunansu, su kuma matasa na bin su da sanduna sannan kuma suna yi musu ruwan duwatsu.

A garin Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya, ita ma a ranar talata an kicime tsakanin wasu ‘yan taadda da masu masu zanga-zanga.

An nuno su rike da karafuna, da suka hada da barandami, tsitaka, fatefate, adduna, takunbba da kuma sanduna.

tui dai suka watsa masu zanga-zangar #EndSARS din.

Haka kuma a a garin Jos ita ma wasu hasalallun matasa sun far wa titunan garin inda suka rika fasa shagunan mutane suna sata.

Za mu biya dukkan bukatun masu zanga-zangar #EndSARS -Gwamnonin Najeriya

Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF), ta bayyana cewa ta rattaba hannun amincewa da dukkan bukatun masu zanga-zangar #EndSARS, kuna za ta magance ko biya musu bukatun domin kara wa gwamnati karsashin gudanar na ingantaccen mulki da gwamnati.

Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya, Kayode Fayemi ne ya bayyana haka a cikin wata takarda da NGF din ta fitar ranar Litinin.

Makonni biyu kenan a kullum masu zanga-zanga na ci gaba da jerin gwano, mamaye manyan titina a Lagos, Abuja da sauran jihohi da dama.

Ko a ranar Litinin din nan masu zanga-zanga sun fita a Kaduna da Kano.

A Abuja kuma sun yi kwanan-zaman-dirshan a bakin harabar Babban Bankin Najeriya (CBN).

Zanga-zangar dai ta rikita harkoki ta kuma tsayar da hada-hada da ayyukan gwamnati a wasu wurare.

Ta kara muni ganin yadda kawowa ranar Litinin mutum 12 ya rasa ran sa a wurin zanga-zanga.

Gwamnatin Tarayya ta amince ta biya wa masu zanga-zanga dukkan bukatun su biyar da su ka nema.

Share.

game da Author