#EndSARS: Abin da na tattauna da Buhari -Gwamnan Legas

0

Gwamnan Legas Babajide Sanwo-Olu ya gana da Shugaba Muhammadu Buhari a kan zanga-zangar da ake ci gaba da yi domin kawo karshen azabtar da jama’a da ‘yan sandan SARS ke yi.

Bayan ganawar ta su, Sanwo-Olu ya zanta da manema labarai a Fadar Shugaban Kasa, inda ya fada musu abin da su ka tattauna da kuma kokarin da shi da sauran gwamnoni ke yi.

Ya ce Buhari ya karbe shi, sun tattauna tsawon lokaci kuma ya damka masa takardar da ke dauke da korafe-korafen matasa, masu neman a rushe SARS baki daya.

“Ni da Shugaba Buhari mun bi wasikar kuma duk mun gamsu da bayanan da matasan su ka yi. Kuma an amince.

“Da Yamma kuma na gana da Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, shi ma ya gamsu da dalilan zanga-zangar da matasa ke yi, har ya ce a saurari bayanin da zai biyo baya.

An tambaye shi yadda za a dawo da martabar aikin dan sanda sai ya ce akwai hanyoyi da dama, ciki har da kara masu albashi.

Mun san dai karin nan ba abu ne da za a yi shi gobe ba. Sai an shigar a kasafin kudi. Amma tabbas za a yi karin.

An yi maganar kafa Gidauniyar Biyan Diyya. To amma dai babu wani adadin kudin da zai iya biyan diyyar ran mutum. Duk da haka, idan aka yi haka din an nuna kulawa, damuwa, tausayi da jinkai ga wanda aka kashe da kuma ga su iyalan sa.

Sanwo-Olu ya ce dukkan Gwamnonin Najeriya na Abuja, sun gana da Buhari, kuma ranar Laraba za su gana da Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Muhammad Adamu.

PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labari da yammacin Talata din nan, yaddq Kwamitin Buhari ya amince a biya dukkan bukatu 5 na masu zanga-zangar rushe SARS.

Taron da Shugaba Muhammadu Buhari ya bada umarni a gaggauta shiryawa a karkashin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, ya amince a biya dukkan bukatu biyar da masu zanga-zangar #EndSARS su ka gindaya wa Gwamnatin Tarayya.

Taron a karkashin Sufeto Janar Muhammad Adamu, ya samu halartar wakilan Hukumar Kare Hakkin Jama’a, Kungiyoyin Kare Hakkin Jama’a da kuma wakilan masu zanga-zanga.

Wasu daga cikin yarjejeniyar da aka amince da ita, sun hada da jami’an tsaro su daina jibgar masu zanga-zanga, kuma a saki dukkan wadanda aka kama.

Kakakin Yada Labarai na Shugaban Kasa, Femi Adesina ne ya turo wa PREMIUM TIMES dukkan abin da aka amince da shi a wurin taron kwamitin.

Jawabin Sufeto Janar Adamu ya jaddada matsayin gwamnati na kyale ‘yan Najeriya su rika yin zanga-zangar lumana, ba tare da gallazawar jami’an tsaro ba.

Sannan kuma ta na kan matsayin ta cewa rayukan ‘yan Najeriya na da matukar daraja. Kuma babban aikin dan sanda shi ne tsare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya.

Sannan kuma za a gaggauta dawo da martaba, kima da darajar aikin dan sanda a kasar nan.

Kuma za a kafa gagarimin kwamiti wanda zai tsara kuma ya shata jadawalin yadda za a sake fasalin bai wa ‘yan sanda horo tun daga mataki na farko har zuwa ka’idojin yadda za su rika bincike da kama wanda ake zargi.

Wakilai da shugabannin kungiyoyin sa-kai na da kare hakki duk sun wakilta, har da Rafsanjani na CISLAC da Kole Shettima daga MAC Arthur.

Akwai kuma wakilin Ma’aikatar Kula da Harkokin ‘Yan Sanda ta Tarayya.

Share.

game da Author