EndSARS: Abdulsalami ya roki masu zanga-zanga su janye daga kan titina

0

Tsohon Shugaban kasa na Mulkin Soja, Abdulsalami Abubakar ya roki masu zanga-zanga su yi hakuri su janye haka nan daga kan riti, domin a samu sararin yin sulhu da kuma lalubo bakin-zaren dukkan matsalolin da ake tayar da jijiyar wuya a kan su, don a samu zaman lafiya da ci gaba mai dorewa a Najeriya.

Da ya ke yi wa ƴan jarida jawabi a gidan sa da ke Minna, babban birnin jihar Neja, ya ce janyewar masu zanga-zanga zai bai wa gwamnatin tarayya damar maida hankali kan biya masu sauran bukatun da su ka nema kuma aka amince za a biya din.

Ya ce tunda har gwamnatin tarayya ta rigaya ta bada hakuri, kuma ta fara biyan wasu bukatun, su ma gwamnonin jihohi sun maida hankulan su kan bukatun da masu zanga-zanga su ka nema a biya masu, to karbe ragamar jagorancin zanga-zangar da wasu ƴan iska su ka yi, ya haifar da mummunar tarzomar da ta haddasa lalata dukiyar gwamnati da ta masu zaman kan su.

Ya ce abin takaici ne yadda abin ya kai ga karya gidajen kurkuku ana balle daurarru masu laifi, kashe jami’an ‘yan sanda da kuma kashe wasu Jama’ar da ba su ji ba, ba su gani ba a sassan kasar nan daban-daban.

“Wannan ya tilasta gwamnati tura jami’an tsaro domin su tabbatar da wanzar da zaman lafiya, bin doka da oda. Hakan kuwa ya kara wa tarzomar haifar da karin asarar rayuka.

“Don haka ina kara rokon matasa masu zanga-zanga su yi hakuri kowa ya tsaida tsrzoma da zanga-zangar, su bada dama a zauna a sasanta kuma a magance matsalolin.”

Share.

game da Author