Mai ba shugaba Buhari shawara kan harkokin tsaro Babagana Monguno ya bayyana wa manema labarai a fadar shugabankasa cewa nan da ‘yan awowi kadan masu zuwa shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai fadi matsayar gwamnati game da tashin hanaklin da ya karade wasu jihohin kasar nan a dalilin zanga-zangar #EndSARS.
Buhari tare da duka hafsoshin tsaron Najeriya, da wasu ministoci da Sufeto janar din ‘yan sanda sun yi ganawa mai tsawo a fadar shugaban kasa inda suka yi masa bayanin abubuwan dake faruwa da yadda kusan harkar tsaro ya tabarbare ya koma hannun yan baranda a wasu sassan kasar nan.
Mungono ya ce shugaban Buhari na can yana nazarin duka abubuwan da aka mika a gaban sa kuma nan da awowi kadan zai fadi matsayar gwamnati da matakan da ta dauka.
Sai dai bai tabbatar da ko Buhari zai yi wa Yan Najeriya jawabi bane kamar yadda wasu suka bukata.
Har zuwa ranar Alhamis, yan Iskan gari suna ta cinnawa wa ofisoshin yan sanda wuta suna sata.
#EndSARS: Yadda sojoji da jami’an kurkuku su ka dakile yunkurin fasa gidan kurkukun Ikoyi a Lagos
Kwanaki uku bayan tserewar daurarru 1993 daga kurkukun Benin a Jihar Edo, sojoji da jami’an tsaron kurkuku sun bude wa wasu daurarru wuta, a yunkurin tserewar da su ka yi daga kurkukun Ikeja da ke Lagos.
Wani da ke tsare a gidan kurkukun da bai yi yunkurin tserewa ba ne ya turo wa PREMIUM TIMES bidiyon yadda daurarrun su ka yi yunkurin guduwa da kuma yadda aka bude masu wuta.
Wannan yunkurin tserewa ya faru ne kwanaki uku bayan da wasu daurarru 1993 su ka tsere daga kurkukun Benin, a jihar Edo.
Majiyar ta cikin kurkukun, ta ce an harbi daurarru da dama a kokarin da su ka yi na balle kofar kurkukun na Ikoyi.
Majiyar PREMIUM TIMES ta ce an Yi rincimi sosai, har sai da ta kai an kira sojoji sun taya jami’an kurkuku dakile boren kokarin tserewar da daurarrun su ka yi.
PREMIUM TIMES ta kira Kakakin Yada Labarai na Hukumar Gidajen Kurkuku ta Kasa, Austin Njoku. An yi rashin sa’a wani ya dauki wayar, ya ce Njoku na cikin taron gaggawa. Amma ya ce zai sanar da shi idan ya fito.
Tun a ranar Litinin PREMIUM TIMES HAUSA ta ruwaito cewa an kafa dokar-ta-baci a Edo, bayan masu zanga-zanga sun fara kirkuku sun saki fursunoni.
Zanga-zangar #EndSARS ta koma tarzoma a Jihar Edo, yayin da masu zanga-zanga su ka fasa gidan kuskuku su ka saki fursunoni a Babban Kurkukun Benin.
Wannan ya tilasta wa Gwamna Godwin Obaseki na Edo kafa dokar-ta-baci tsawon awa 24, domin kokarin shawo kan lamarin.
PREMIUM TIMES ta gano cewa matasa ne su ka karbe ragamar zanga-zangar su ka kutsa su ka saki wasu daurarrun cikin kurkukun.
Matasan wadanda sun kai 100, wasun su day yawa sun samu raunuka ya yin da su ka yi arangama da artabu tsakanin su day jami’an tsaron kurkukun, wadanda aka ce sun rika harba bindigogi.
Discussion about this post