Jihar Legas da wasu jigohin Kudu Maso Yamma na cigaba ganin tashin hankali, a yau Laraba tun bayan rikidewar zanga-zangar #EndSARS zuwa wani abin da ban.
Tun da safiyar Laraba hasalallun matasan suka rika bi ma’aikatun gwamnati da caji ofis din ƴan sanda suna cinna musu wuta.
Da farko dai sun fara ne cinna wa tarin manyan motocin haya da mallakin gwamnatin Legas, daga nan sai suka dira gidan sarkin Legas, nan ma suka banka mata wuta, bayannhaka suka dunguma ginin hukumar kula da tashoshin ruwan Najeriya, nan ma suka banka mata wuta.
Matasan suka cigaba da bi manyan ma’aikatun gwamnatin jihar suna konawa.
Sun babbake kusan duka ofishishin ƴan sandan jihar Legas sannan kuma duk wanda suka kama tasa ta kare, da na sai barzahu.
Suna bi musamman suna babbanka wa duk wata kadara da suka sani mallakin tsohon gwamnan jihar ne, Bola Tinubu. Tun da farko dai matasan sun cinnawa kamfanin talbijin din sa mai suna TVC, daga nan sai suka garzaya kamfanin jaridar Nation wanda mallakin sa ne ita ma suka banka mata wuta.
Haka kuma a jihohin Oyo da Ogun har da Ondo, matasan garuruwan na bi na cinnawa ma’aikatun gwamnati wuta da kamfanoni.
Komai ya tsaya cak a kasar yanzu inda kowa ta kansa ya ke yi musamman a yankunan kudu maso yamma da kudu maso gabashin kasar nan.