#EndSARS: Ƴan Arewa Shashashu ne, sun bari malamai na ta hure musu kunne – Inji Buba Galadima

0

Jigon Adawa a Najeriya, Buba Galadima ya bayyana cewa ƴan Arewa Shashashu ne da suke kasa kunne suna sauraren malaman dake cewa zanga-zangar #EndSARS ta kabilanci ne da addini.

A hira da yayi da sashen Hausa na BBC, Buba Galadima ya ce da kansa ya hangi masu zanga-zangar #EndSARS suna tattakin su salin-alin suna tafiyar a gefen titi a Abuja kullum ko titin ba su hawa saboda natsuwa da kamala, amma kuma sai ga wasu wai da ake zato daga wasu jihohi aka kawo su sun tarwatsu su.

Galadima ya ce ire-iren kiraye kirayen da malamai suka rika yi na cewa ƴan Arewa su kaurace wa zanga-zangar da yi musu hudubar cewa akwai wata shiri dabam a cikin wannan tafiya bai dace ba.

” Ni da kaina na gansu a Abuja, suna zanga-zangar su na #EndSARS, basu tsangwami kowa ba, basu zagi kowa ba, basu ma tare hanya ba, suna gefen titi ne abinsu. Daga baya sai wasu suka shigo da ake zargi daga wasu jihohi aka dauko su, dauke da gariyo da barandami suka kai wa masu zanga-zangar farmaki.

Daga nan sai yace dole a daina nuna kiyayya ga ƴan kudu saboda idan ba haka ba ida suka dare kujerar shugabancin Najeriya zasu iya ci wa Arewa mutunci suma.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi jawabi ga ƴan kasa a ranar Alhamis inda ya yi kira ga masu zanga-zanga su hakura su janye daga titunan kasar nan.

Ya ce gwamnati na bin bukatunsu daki daki kuma za a biya su duka.

Share.

game da Author