Majalisar Kolin Shari’a ta Najeriya (SCSN), ta yi kakkausan zargi ga Amurka, Birtaniya da kuma Canada cewa ta na saurin yanke hukuncin nuna bambanci da ɓangaranci ga Musulman Najeriya, ba tare da ta bibiye bangarorin biyu ta ji ta bakin kowane ba.
Wannan zargi ya fito a cikin wani jawabin da kungiyar ta yi wa manema labarai a Abuja.
“Mun damu kwarai dangane da irin yadda Birtaniya, Amurka, Kanada da wasu kasashe ke nuna bambanci da ɓangaranci sauraren bangare daya a kasar nan, ba tare da bin diddigin tantance gaskiyar lamari ba.”
Muhammad Bin-Usman ne ya karanta takardar, a madadin sauran mambobin kungiyar da su ka hada da Nafi’u Baba-Ahmad, kungiyar ta yi kira su rika rashin bambanci da daukar bangaranci wajen zartas da wani hukunci ko daukar wata matsaya da ta shafi Najeriya.”
Kasashen Amurka, Birtaniya da Kanada sun fito sun yi tir da bude wa masu zanga-zanga wuta da sojoji su ka yi.
Sai dai kungiyar ta xe zanga-zangar #EndSARS ta tashi daga ta kishin kasa ta rikide ta kabilanci da addinanci, saboda kasassaba da sakin-baki da kazaman kalaman da wasu shugabannin kiristoci su ka rika furtawa.”
Sai dai kuma bai ambaci sunan kowane limamin coci daya ba.
Ya ce saboda kazaman kalaman da shugabannin kiristoci su ka rika yi, hakan ya haddasa kai wa kadarori da dukiyoyin musulmi hari a wasu gaduruwa.
SCSN ta bada misalin garuruwan da aka kai wa kadarorin musulmi hari da su ka hada da Apo a Abuja, Dutsen Alhaji, Fatakwal, Sabon Gari Kano, Aba, da kuma wurare a Lagos.
“An kai wa Musulmi hari a Jos, har an lalata Jaiz Bank, wanda bankin Musulunci ne. An lalata wurare a Kano, har da sabon katafaren kantin Galaxy Mall a Kano.
Bin-Usman ya yi kira ga manyan kasashen duniya su rika adalci ba nuna bbangaranci ba.
Ya yi kira ga gwamnati ta tashi tsaye wajen cika nauyin da dokar kasa ta wajabta mata na kare rayuka da dukiyar jama’a.