Tun ana ganin kamar za a gama yau, gobe, yau gobe ga shi yanzu yana neman yafi karfin gwamnati da mutanen kasa Najeriya idan ba tashi tsaye aka yi ba.
Saboda wasu tsiraru sun nuna cewa ga yadda suke so dole abi kuma. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya saka hannu ya amince da bukatun su amma kuma suka yi wa gwamnati kunnen uwar shegu, babu abinda ya dame su, an kyale su sai cin karen su ba babbaka su ke sauran mutane kuma ko oho.
Ba a taba gwamnati wanda da ga yin kira ta amsa cikin gaggawa irin wannan gwamnati ba. Amma kuma bai haifar mata da ɗa mai ido ba duk ta biya musu bukatun.
Yanzu dai kiri-kiri kowa ya sani kuma ya gani cewa wannan zanga-zanga bata da alfanu a kasar nan. Abin ya koma har tsiraici suke nunawa, suna zage-zagen manya da shugabannin amma kuma babu wani da ya isa ya ce musu ga yadda za suyi ko su bi. A kullum sai suce ga yadda suke so, kuma an zura musu ido ana kallon su da sunan ƴancin ɗan Adam.
Babban abinda ake so a tabbatar a kasar nan ta hanyar wannan zanga-zanga sune a ƙaƙaba wa mutane ajandodin kasashen turai da wasunsu ke narka wa wadanda suka shirya wannan zanga-zanga kudade, Ajandodi irin su a fifita mata a kan maza, wato ƴancin da mace za ta iya fekerewa, tsegeranci da rashin kunya, da yi wa mazan auren su fitsara, baiwa ƴaƴa ƴanci yi wa iyayen su rashin kunya da lalata dabi’ar mutane.
Dole shugabannin Arewa su tashi tsaye su maida hankalin su wajen gane cewa wannan abu ba shi da alfanu ga mutanen yankin Arewa gaba daya.
Kada su kuskura su biye wa mutanen kudu da ajandodin su wanda turawa ne wanda shiri ne na tarwatsa Arewa da kasar baki daya.
Wannan zanga-zanga na #EndSars ya wuce yadda ake tsammani fa. Har daga kasashen waje ana mara musu baya da basu gudunmawar kudade domin samun nasara a wata ajanda taso da suka saka a gaba.
Discussion about this post