Gwamnan jihar Kaduna ya nada Magajin Garin Ahmed Bamalli sabon sarkin Zazzau.
Bamalli shine sarki na farko daga bangaren Mallawa, wanda suka yi sarautar Zazzau fiye da shekaru 100 da suka wuce tun bayan rasuwar kakan sa Aliyu Dan Sidi.
Ahmed Bamalli, kwararren dan Boko ne kuma ma’aikacin gwamnati. Mahaifin sa ya ya rike ministan harkokin kasashen waje a jamhuriyya ta farko.
Gwamnatin Kaduna ta yi masa murna sannan ta yi masa addu’an Allah ya taya shi riko.