Duk da rusa rundunar SARS da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi, da jadda kokarin gwamnatin sa na tabbatar da an kawo sauye-sauye a rundunar ƴan sandan kasar wanda shima mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo yayi, ƴaƴan su Zara Buhari da ƴar mataimakin sa Kiki Osinbajo duk sun bi ayarin masu yin zanga-zanga da asoke rundunar.
Zara Buhari da Kiki Osinbajo sun sassaka hotuna dauke da rubutu da tambarin a soke wannan sashe na ƴan sanda sannan a kawo karshen muzguna wa ƴan Najeriya da ƴan sanda ke yi a koda yaushe.
Sai dai ita Zara nata bai dade ba, ta yi maza maza ta cire a shafinta ta Instagram.
Idan ba a manta ba Shugaba Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, gwamnati ta saurari kukan ƴan Najeriya da kunne bibiyu, wanda a dalilin haka ta rusa rundunar SARS din kuma ta tsara yanyoyi da za a bi don ganin ba a sake komawa gidan jiya ba.
Buhari ya ce baya ga rusa wannan bangare na ƴan sanda za aci gaba da yi wa rundunar garambawul domin a gina rundunar ƴan sanda mai nagarta wanda ya san ƴanci da kare hakkin ƴan kasa.
Har yanzu dai ana cigaba da zanga-zangan a wasu jihohin kasar nan da ya hada da jigar Legas, Osun da Ogun sannan kuma abin ya dan kazanta, da har ana samun rahotannin kisan mazu zanga-zanga.
Discussion about this post