Dalilin da ya sa gwamnonin Arewa basu tare da masu zanga-zangar #EndSARS

0

Shugaban ƙungiyar gwamnonin Arewa, Simon Lalong, kuma gwamnan jihar Filato ya bayyana rashin jin dadin gwamnonin yankin kan rushe rundunar SARS da gwamnatin Tarayya ta yi.

Idan ba a manta ba har yanzu tsirarun matasa musamman a yankin kudancin Najeriya na ci gaba da gudanar da zanga-zangar #EndSars.

Duk da gwamnati ta amince da bukatun masu zanga-zangar, har yanzu sun ci gaba da fitowa manyan wasu titunan biranen Najeriya.

A taron gwamnonin Arewacin Najeriya 19, dukkan su sun nuna rashin jin dadin su kanbyadda shugaban ƴan sanda ya rushe rundunar Sars din.

” Mu a yankin Arewacin Najeriya, muna matukar kinjinawa rundunar Sars din min suna yi mana aiki a yankin.

” Dama kuma dole a samu baragurbi a cikin su amma kuma maimakon a rushe rundunar kamata yayi a yi mata garambawul ne, a tsintsince wadanda lalatattu ne a zubar sa su sai kawai aka rushe su

” Wannan abu bai yi mana dadi ba kuma bamu tare da masu wannan zanga-zanga.

Gaba dayan su gwamnonin sun yi kira ga Buhari da ya sake duba wannan abu domin a gyara.

Idan ba a manta ba, Majalisar Jihar Barno ta karrama babban jagoran SARS na jihar, Muhammad Ibrahim.

Sun bayyana cewa karramawar sa Majalisa ta yi masa, an yi ta he bisa jajircewar kwazo da sadaukar da kan sa wajen wanzar da zaman lafiya a jihar Barno.

Ya yi Kwamandan Tarwatsa ‘Yan Fashi a Jihar Lagos, kafin a maida rundunar zuwa SARS cikin 2011.

Shugaban Masu Rinjaye Dige Muhammad daga Karamar Hukumar Kala Balge ne ya daga hannu kuma ya nemi a kakkama babban san sandan.

Kwamanda Ibrahim ya gode wa al’ummar jihar Barno, bisa karramawar da su ka yi masa.

Idan ba a manta ba, a ranar Talata PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin da masu zanga-zanga a Maiduguri su ka bayyana cwa “SARS na yi mana matukar amfani a Barno.

Wasu masu zanga-zanga a Maiduguri, babban birnin Jihar Barno, sun fito kan titi su na nuna rashin amincewa da rushe ‘Yan Sandan Gaggawar Dakile Fashi da Makami ba, wato SARS.

SARS, wadanda a Turance ake kira da Special Anti-Robbery Squard, an rushe su a ranar Lahadi, bayan da zanga-zanga ta yi tsanani a wasu manyan garuruwan kasar nan, ana kiraye-kirayen rushe su.

Masu zanga-zanga sun nuna gajiyawa da irin yadda jami’an SARS ke wuce gona da iri, wajen azabtar da mutane da kisa ba bisa tsarin da dokar kasa ta gindaya ba.

Sai dai kuma a jihar Barno, wasu fitowa kan titi su ka yi, domin nuna rashin goyon bayan rusa SARS da aka yi.

Share.

game da Author