CUTAR KORONA: Masu komawa ci gaba da harkokin noma sun fi masu komawa sauran kasuwanci yawa – NBS

0

Dimbin manoma sun koma ci gaba da harkokin noma musamman a cikin watannin Juli da Agusta, kamar yadda binciken Kididdigar da Hukumar Kididdigar Alkaluman Bayanai ta Kasa (NBS) ya nuna.

NBS ta yi wannan rahoto ne bayan kammala kididdige tasirin da cutar korona ya yi a cikin al’umma, rahoto na hudu.

Bayanan na NBS sun nuna cewa an samu gagarimin karuwar komawar manoma ci gaba da harkoki ne saboda watannin Yuli da Agusta, lokutan fara girbin wasu amfanin gona ne.

“Duk da cewa wasu harkokin kasuwanci an bude su tun bayan barkewar cutar Korona, to amma su harkokin sake yin tsaye cak su ka yi a cikin watannin Yuli da Agusta.” Cewar NBS.

Hukumar NBS ta kara da cewa ya zuwa cikin Agusta, kashi 35 bisa 100 ne na gidajen da ke harkokin da ba su shafi noma ba su ka iya ci gaba gudanar da kasuwancin su cikin 2020, tun daga Afrilu da Mayu. Adadin ya yi kasa daga kashi 40 bisa 100 a cikin watan Yuli.

Rahoton ya kara da cewa kashi 13 bisa 100 ne su ka ci gaba da harkokin su a cikin watan Yuli, amma kuma kashi 12 ne su ka ci gaba bayan watan Yuli.

Rahoton ya ce kashi 54 na masu harkokin kasuwancin dabbobi ne su ka ajiye dabbobin su tun daga tsakiyar Maris.

Cutar Korona ta shafi kusan kashi 36 bisa 100 na gidajen da ake kiwon dabbobi.” Cewar rahoton.

Gidajen da suka sha wahalar ciyar da dabbobin su a lokacin Korona, sun kai kashi 89 na yawan gidajen masu kiwon dabbobi. Yayin da kashi 79 kuma su ka kasa samun sukunin samun magungunan kare lafiyar dabbobin na su.

Kashi 17 bisa 100 na gidajen da ake kiwon dabbobi sun sayar da dabbobin su a lokacin korona. Kuma bincike ya nuna cewa korona din ce ta sa su sayar da dabbobin. Amma da babu barkewar cutar, to ba za su sayar da dabbobin ba.

“Sayar da dabbobi sanadiyyar barkewar cutar Korona, ya fi kamari a gidajen marasa galihu.

“Matsalar rashin abinci ce ta haifar da haka, domin abincin ya yi karanci fiye da yadda Rahoton GHS-Panel ya fara nunawa a watannin Yuli da Agusta.”

Share.

game da Author