Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 62 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Lahadi.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Lahadi sun nuna Kamar haka; Taraba-18, Ogun-15, FCT-6, Kaduna-6, Katsina-4, Ondo-4, Ekiti-3, Rivers-3, Kano-1, Osun-1 da Sokoto-1.
Yanzu mutum 61,992 suka kamu da cutar a Naj eriya, mutum 57,465 sun warke, 1,130 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 3,397 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 20,789, FCT –5,967, Oyo – 3,421, Edo –2,648, Delta –1,812, Rivers 2,773, Kano –1,742, Ogun – 2,010, Kaduna –2,617, Katsina -952, Ondo –1,666, Borno –745, Gombe – 883, Bauchi – 710, Ebonyi –1,049, Filato -3,587, Enugu – 1,314, Abia – 898, Imo – 614, Jigawa – 325, Kwara – 1,067, Bayelsa – 403, Nasarawa – 478, Osun –922, Sokoto – 165, Niger – 274, Akwa Ibom – 295, Benue – 486, Adamawa – 252, Anambra – 277, Kebbi – 93, Zamfara – 79, Yobe – 79, Ekiti – 332, Taraba- 122, Kogi – 5, da Cross Rivers – 87.
Matakai 11 da makarantu za su kiyaye don kare ƴan makaranta daga kamuwa da cutar korona.
Idan ba a manta ba a watan da Satumba ma’aikatar ilimi ta sanar cewa gwamnatin tarayyar ta amince wa gwamnonin jihohin kasar nan su tsaida ranar bude makarantu a kasar nan.
A watan Maris ne gwamnati ta rufe duka makarantun kasar nan a dalilin barkewar annobar Korona a kasa Najeriya da Duniya.
Zuwa yanzu jihohin Legas, Kano, Kaduna Barno, Ogun ,Ekiti da wasu jihohi duk sun sanar da ranakun bude makarantu, wasu ma har sun bude su.
Sai dai kuma dole makarantu su yi taka tsantsan wajen samar wa yara kariya ta hanyar wadata su da abubuwan da ake tsaftace jiki da kuma karantar da su hanyoyin samun kariya a duk lolacin da suka tunkari makaranta.
Ga matakan
1. Makarantu su tabbatar duk wanda zai shiga makaranta sai an yi masa gwajin Korona sannan a duba yanayin zafin jikin sa.
2. A tabbatar duk Wanda zai shiga makaranta ya saka takunkumin fuska.
3. Makaranta ta kebe wasu wurare a makarantar da za a rika wanke hannaye da ruwa da sabulu domin dalibai, malamai da ma’aikatan makaranta.
4. Makarantun kwana su samar da wurin yin gwajin cutar sannan da wurin kebe wadanda tsautsayin kamuwa da cutar ya afka musu.
5. Makarantu zu kebe wuraren da za a kwantar da wani Koda ya kamu da cutar a makarantan.
6. Horas da ma’aikatan lafiya na kowanne makaranta kan yadda za su kula da wadanda suka kamu da cutar tare da Samar wa ma’aikatan kayan kariya.
7. Makaranta za ta nemi izinin iyaye domin kwantar da dalibi koda wani cikin su ya kamu da cutar.
8. Makarantu su tabbata suna kula da tsaftace muhallin su akai akai sannan a watadar da fankoki a ajujuwa domin samun wadatar iska
9. Ajujuwan da ba za a iya saka musu fankoki ba, a tabbata an bude windina domin iska ya riga zagayawa.
10. A rage cinkoson yara a Ajujuwa, sannan a saka su a tsakanin juna da tazara kamar ta mita 1 zuwa 2.
11. Baya ga ruwan wanke hannu, yana da kyau a wadata kowani aji da man tsaftace hannaye. Wanda a duk lokacin da aka dawo daga hutun rabin lokaci, sai dalibi ya goga a hannun sa kafin ya zauna a kujera.