Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 119 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Litini.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Litini sun nuna cewa jihar Legas ta samu karin mutum –77, FCT-26, Filato-9, Edo-4, Oyo-2 da Nasarawa-1
Yanzu mutum 62,111 suka kamu da cutar a Naj eriya, mutum 57,571 sun warke, 1,132 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 3,408 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 20,884, FCT –5,993, Oyo – 3,425, Edo –2,652, Delta –1,812, Rivers 2,773, Kano –1,742, Ogun – 2,010, Kaduna –2,617, Katsina -952, Ondo –1,666, Borno –745, Gombe – 883, Bauchi – 710, Ebonyi –1,049, Filato -3,603, Enugu – 1,314, Abia – 898, Imo – 614, Jigawa – 325, Kwara – 1,067, Bayelsa – 403, Nasarawa – 479, Osun –922, Sokoto – 165, Niger – 274, Akwa Ibom – 295, Benue – 486, Adamawa – 252, Anambra – 277, Kebbi – 93, Zamfara – 79, Yobe – 79, Ekiti – 332, Taraba- 122, Kogi – 5, da Cross Rivers – 87.
Yaran Makaranta 181 da malamansu sun kamu da Korona a wani makaranta a Legas
Akalla dalibai da malaman su 181 ne aka tabbatr sun kamu da Korona da wani makaranta mai zaman kansa a Legas.
Ma’aikatar kiwon Lafiya ta jihar Legas ta sanar cewa yaran makaranta 181 da wasu malaman su sun kamu da Korona a wani makarantar Kwana dake Lekki, Jihar Legas.
Kwamishinan Lafiya na jihar Akin Abayomi, ya shaida cewa bincike da aka gudanar ne ya sa aka gano wadanda suka kamu da cutar.
” Wata daliba ‘yar ajin SSII ce ta fara rashin Lafiya, da aka kaita asibitin makarantar, a nan ne aka gano ta Kamu da Korona. Da aka yi wa daliban makarantar gwaji sai aka gano yara 181 duk sun kamu da wasu daga cikin malaman su.
” Sai dai cutar bata kwantar da su ba dukkan su. Mun shawar ce su da su cigaba da zama a makarantar kada kuma su koma gida su yada cutar, sannan kuma mun tura malaman lafiya su ci gaba da samar da kula a wurin da kewaye.”