Likita dake koyarwa a makarantar koyar da aikin malunta dake Ibadan Adekoya Owosibo ya hori mutane da su rika cin akalla kwai kwaya daya tal a duk rana cewa yin haka na inganta kiwon lafiyar mutum.
Adekoya ya fadi haka ne ranar Juma’a a Ibadan a hira da yayi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriyaa wajen taron sanin abincin da ya fi dacewa mutane su rika ci.
Adekoya ya kara da cewa rahoton binciken cibiyar ‘British Heart Foundation’ ya tabbatar cewa cin kwai baya sa mutum ya kara kiba a jiki sai dai ma ya inganta lafiyar sa.
Adekoya ya ce bincike ya nuna cewa sinadarin inganta kiwon lafiya dake kwai guda daya kusan dai–dai yake da sinadarin dake cikin nonon uwa.
Bayan haka tsohon sakataren kungiyar masu kiwon kaji reshen jihar Oyo Olugbenga Ogunwole ya koka da matsalolin da masu kiwon kaji ke fama da su a kasar nan duk da cewa su ke samar da kwan da ake ci a kasar.
Ogunwole ya yi kira ga gwamnati da ta tsara hanyoyin inganta fannin aiyukkan noma tare da kawar da matsalolin da masu kiwon kaji ke fama da su a Najeriya.
Ya ce inganta aiyukkan noma zai taimaka wajen inganta tattalin arzikin kasar.
Idan ba a manta ba a watan Mayu ne Kungiyar masu kiwon kaji ta kasa ta yi kira ga mutane da su rika cin kwai a kullum ranar domin inganta karfin garkuwan jikin su.
Kungiyar ta ce samun karfin garkuwan jiki zai taimaka wajen kare mutum daga kamuwa da cututtuka musamman cutar Koronabairos da ya zama annoba a duniya.
Discussion about this post