Buhari ya zargi gwamnatocin Obasanjo, Yar’Adua da Jonathan kan halin kakanikayi da Najeriya ta samu kanta a ciki da yake kokarin fidda ta

0

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya zargi gwamnatocin baya tun daga 1999-2015 cewa sune suka saka Najeriya cikin halin kakanikayi da ya sa har yanzu ana fafutikar yadda za a fiddo ta ne daga wadannan matsaloli ne wanda gwamnatin sa ke yi ba dare ba rana.

” Wadanda suka shugabanci Najeriya daga 1999-2015, suka gurgugunta ne wai yanzu ke da bakin cewa bamu yin wani abin a zo a gani ba a mulkinmu.

Buhari ya ce gwamnatin sa na aiki ba dare ba rana domin dawo da martabar Najeriya da bunkasa tattalin arzikin kasan.

Shugaba Muhammdu Buhari ya yi tilawar musabbabin shigar Najeriya matsalolin da ta tsince kan ta a ciki, ko aka jefa ta, tare da yin kiran cewa sai an taru an hada kai za a iya tsire tare.

A jawabin sa na cikar Najeriya shekaru 60, Buhari wanda ya yi jawabi daga Fadar Shugaban Kasa, ya ce, “tilas sai mun waiwayi baya, yadda mu ka tsinci kan mu a inda mu ke a yanzu, kafin mu iya dafa tudun-mun-tsira.”

Buhari, wanda a farkon jawabin sa ya kara jaddada godiyar sa ga ‘yan Najeriya, bisa gaskata shi da su ka yi har su ka damka masa amanar mulki zango biyu, ya fara waiwaye yadda Najeriya ta ke a lokacin da a ka samu ‘yanci, a 1960.

“Lokacin da aka samu ‘yanci a 1960, adadin ‘yan Najeriya ba su wuce mutum milyan 45 ba. A cikin mu din ma, milyan 7 ne kadai ke zaune a birane. Saura duk a karkara da kananan garuruwa su ke.

“Amma a yau yawan mu ya kai sama da mutum milyan 200. Kuma kashi 52% na yawan wadannan mutane (wato mutum milyan 104) duk a birane ko garuruwa su ke zaune.

“Idan mu ka dubi yadda iyayen kasar masu kishi su ka gina kasa bayan sun kwato mata ‘yanci, to sai mu dubi kan mu. Shin mun yi gaskiya da kishi da rikon amana, kamar yadda na bayan mu din su ka yi?” Inji Buhari.

Daga nan ya fara kawo wadansu cikas din da Najeriya ta fara cin karo da su bayan samun ‘yanci.

Buhari ya bayyana cikas irin su Yakin Basasa da aka yi watanni 30 ana fafatawa. Sai kuma shekaru 29 da Najeriya ta shafe a karkashin mulkin soja.

“Haka nan da tafiya ta yi tafiya, tsarin ma’aikatan gwamnati, ‘yan sanda, alkalai da sojoji sun sun tabarbare.

“Don haka tilas sai mun fara warkar da mikin da ke jikin kasar nan domin su tsira daga halin da ake ciki.

“Najeriya fa ba Shugaban Kasa ne ke da ita, ko shi ko ‘yan adawa ba. Ta kowa ce. Saboda haka kowa ya tashi tsaye, aiki ne na mu baki daya.” Inji Buhari.

Daga nan sai ya koma ya fara jero wasu ayyukan ciyar da al’umma gaba da ya ce gwamnatin sa ta samar, ciki har da su TraderMoni, Shirin Samar da Aiki Ga Mutum Milyan 100 nan da shekaru 10 da sauran su.

Share.

game da Author