Gwamna Aminu Tambuwal na Jihar Sokoto, ya ce kafin Najeriya ta shawo kan manyan kalubalen da su ka dabaibaye kasar, tilas sai an kawar da fatara da rashin aikin yi tukunna.
Tambuwal ya yi wannan bayani a ranar Alhamis, a Abuja, wurin kaddamar da “Shirin Inganta Rayuwa Na Mutum Milyan 20.”
‘Project 20 Million’, shiri ne don fito da ‘yan Najeriya tantagaryar mutum milyan 20 masu kyakkwyawan ra’ayi da muradin tabbatar da ingantacciyar gwamnati, shugabanci sahihi wanda zai maida kasar nan kasaitacciya.
Tambuwal, wanda Mataimakin sa na Musamman a Harkokin Kanana da Matsakaitan Masana’antu, Akibu Dalhatu ya wakilta, ya ce kafin Najeriya ta samu wanzuwar zaman lafiya, tilas sai an kawar da wadancan kalubale da matsalolin da ya yi magana a baya.
Ya ce sai gwamnati ta kawar da fakiranci da rashin aikin yi, sannan jama’a za su fara ji a jikin su cewa akwai gwamnati mai kula da su.
Tambuwal ya ce duk da wadannan matsaloli da ake fuskanta, Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kokari sosai wajen fito da tsare-tsaren bunkasa rayuwar marasa galihu.
Sai dai kuma ya ce tilas sai gwamnati ta rika shigar da jama’a wajen ayyukan gudanar da kasafin kudi, maimakon a bar shi kacokan a koda yaushe a hannun jami’an gwamnati.
“Hakan zai sa a samu gagarimar gudummawa daga bangaren jama’a, wadanda kuma ta haka za su bayar da shawara kan bangare, da wuraren da ya zama wajibi a fi bayar da fifiko wajen aiwatar da ayyukan raya Kasa.
“Idan aka tsarma jama’a cikin ayyukan kasafin kudi, hakan zai sa su rika sa-ido, su tabbatar ana ayyuka bisa gaskiya, kuma su ga cewa ba a karkatar da kudaden kwangiloli ko fara aiki a watsar , bayan an karbi kudi ba.” Inji Tambuwal.