Shugaba Muhammdu Buhari ya amince a kashe naira bilyan 10 wajen aikin shata kan-iyakoki a Kananan Hukumomi 546 a kasar nan.
Aikin wanda aka fi sani da Enumeration Area Demarcation (EAD), ya na cikin shirin kidayar adadin al’ummar Najeriya arankatakaf da za a yi ba da dadewa ba.
Gwamnatin ta tsara aikin shata tantance iyakokin ne domin a ji saukin gudanar da kidayar.
A bangaren kidayar, Buhari ya kuma amince da kara naira bilyan 4.5 cikin kasafin 2021, domin a kammala aikin tantancewar, wanda shi ne sharar-hanyar aikin kidayar da za a fara gadan-gadan.
Shugaban Riko na Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC), Eyitayo Oyerunji ne ya bayyana haka ranar Litinin, a Abuja.
“Cikakkun bayanan abin da aikin EAD ke samarwa, abu ne mai marukar muhimmanci ga aikin sa-ido da jami’an tsaro ke gudanarwa da kuma afkuwar manya da kananan laifuka a yankuna daban-daban.” Inji Oyetunji.
“Shugaban Kasa ya kara wa wannan shiri karfi ta hanyar kara naira bilyan 45 cikin Kasafin 2021 domin kammala shirin, wanda sharar-hanya ce ga aikin kidayar da za a gudanar.” Inji shi.
Da aka tambaye shi ko yaushe ne za a fara aikin kidayar, sai ya ce har yau ba a sa ranar farawa ba.
Amma dai ya ce hakan alamu ne tabbas da ke nuna cewa nan ba da dadewa ba za a fara aikin kidayar.
Rabon da a kidaya ‘yan Najeriya tun cikin 2006.
Oyetunji ya ce an rigaya an kammala aikin shata tantance kananan hukumomi 228 a fadin jihohin Najeriya 36 da Gundumar FCT Abuja.
Ya ce za a ci gaba da aikin shata iyakokin kashi na 10 daga ranar 5 zuwa 29 Ga Oktoba. Kuma akwai aikin bada horo ga ma’aikatan da za a dauka da kuma fita ana aiki wurjanjan.