Shugaba Muhammdu Buhari ya ce daga yau ya zama tsarin gwamnatin tarayya cewa akwai aiki na jiran duk wanda ya kammala digirin koyarwa da kuma kudin kashewa.
Ministan Ilmi Adamu Adamu ne ya bayyana wannan albishir a wurin Taron Ranar Ilmi ta Duniya, ranar Litinin a Abuja.
Shugaba Buhari kuma ya kara wa malamai albashi, ya kara masu shekarun wa’adin yin ritaya daga tsawon shekaru 35 ana aiki zuwa shekaru 40.
A ranar Litinin ce Minista Adamu ya bayyana rattaba hannun amincewa a kara wa malaman makaranta albashi.
Wannan ya na cikin sakon sa na Ranar Malaman Makaranta ta Duniya (World Teachers Day) a Abuja.
Ministan Harkokin Ilmi, Adamu Adamu ya wakilci Buharia wurin taron, inda ya kara albishir din cewa an kara wa malaman wa’adin dadewa ana koyarwa kafin a yi ritaya, daga shekaru 35 ana aiki zuwa shekaru 40.
Buhari ya ce an yi karin domin a kara karfafa wa malaman makaranta karfin guiwar koyarwa a wannan mawuyacin halin annobar cutar korona da ya addibi duniya.
Wannan kari ya zo daidai lokacin da Gwamnatin Tarayya ke tabka kirimirmirar rikici a kan batun biyan albashi a karkashin tsarin ‘yar keke-da-keken biyan albashi, wato IPPIS.
A yanzu dai gwamnati ta bayyana ranar komawar ‘yan makarantar firamare da daliban sakandare.
Sai dai ba gaba dayan su ne za su koma lokaci daya ba.
Ya ce malamai ne ke da karfin iya sauya tunanin kananan yara su zama masu kwakwalwar da a gaba al’umma gaba daya za su amfana da su.
“Malamai ne kadai ka iya samar da al’umma tagari, tw hanyar kyankyashe dalibai masu kaifin kwakwalwa da nagartaccen ilmin da za su iya maida kasar mu kasaitacciya nan gaba.”
Buhari ya kara da cewa abu mai muhimmanci ne kuma gwamatin sa ta samar da bigire na horas da malamai su zama kwararru sosai.
“Za a fadada Gasar Raba Kyautukan Cancanta Ga Kwararrun Malamai ta Shekara domin a hada wasu fannonin koyarwar da malamai su ka yi bajinta.
“Za a rika bada kyautar Gwarzon Shugaban Makaranta, Gwarzon Malami a Makarantun Gwamnati, Gwarzon Malami a Makarantun Kudi da sauran su.
Olaoluwa Asibiojo ne ya zama Gwarzon Malami daga Amoye Grammar School a Ikere, Ekiti, Jihar
Ekiti. Sai Istifanus Caroline ta zama Gwarzuwa Malaman Makarantun Kudi daga Makarantar L Crawford ta Cocin ECWA da ke Kaltungo, Jihar Gombe.
A jawabin sa, Shugaban Kungiyar Malamai ta Kasa (NUT) Nasir Idris, ya ce karin mafi kankantar albashi na naira 30,000 ma har yau wasu jihohi da Babban Birnin Tarayya, Abuja ba su ba su ma fara aiki da shi ba.
Ya ki kiran Gwamnatin Tarayya ta gaggauta fara cika alkawurran baya.
Duk da haka, yawancin malaman da PREMIUM TIMES ta zanta da su, sun yi murna da wannan umarnin karin albashi da Buhari ya ce za a yi musu da kuma kara musu shekaru biyar na wa’adin ritaya, daga 35 zuwa 40 ana aiki.