Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya aika da sakon taya murna ga sabon sarkin Zazzau maimartaba Ahmed Bamalli.
” Yanzu ka kafa tarihi, gidan sarautar da ka fito wato gidan Mallawa sun shekara 100 rabon su da su hau wannan kujera ta sarautar Zazzau.
” Ina taya ka murna sannan ina kira gareka da ka hada kan gidajen sarautan zazzau gaba daya. Ina fatan Allah ya taya ka riko ya baka ikon rike al’ummar ka da gaskiya da kuma rikon Amana.
Sanar da sabon sarkin Zazzau ke da wuya, sai Yeriman Zazzau, kuma wanda shima ya nemi kujerar sarautar Zazzau din ya mika sakon taya murbna ga sabon Sarkin Zazzau Ahmed Bamalli.
Mannir wanda dan tsohon sarkin Zazzau, Ja’afaru Dan Isyaku ne ya yi wa sabon sarki fatan Alkhairi da rokon Allah ya taya shi riko.
Idan ba a manta ba Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya sanaran da zabin Magajin Garin Zazzau Ahmed Bamalli sabon sarkin Zazzau ranar Laraba.
Garin Zariya ya barke da murna a lokacin da sabon Sarki ya isa fada bayan sanarwan.