BIDIYO: Murna ya barke a Zariya bayan nada sabon Sarkin Zazzau Ahmed Bamalli

0

Bayan sanar da nadin sabon sarkin Zazzau Ahmed Bamalli, garin Zazzau ta cika da farin ciki da murna, inda ake ta kabbarori ana yi wa sabon sarki fatan Alkhairi da yi masa addu’o’in Allah ya taya shi riko.

Idan ba a manta ba, da safiyar Laraba ne gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da nada sabon Sarkin Zazzau Ahmed Bamalli, sarki na 19 a masarautar Zazzau.

Mutane sun yi cincirindo a fadar suna zuwan isowar sabon sarki.

Isar sa ke da wuya kuwa sai aka fara murna ana kabbarori.

Share.

game da Author