Bankin Lamuni na Duniya (IMF), ya kara wa kasashe 28 wa’adin biyan basussuka sakamakon halin kaka-ni-ka-yi da cutar korona ta jefa duniya.
Haka nan kuma akwai dalilin cewa kasashen su na sahun kasashen da tattalin arzikin su ke kakarin numfasawa da kyar, saboda dannewar da korona ta yi wa tattalin arzikin duniya.
An kara kasashen 28 wa’adin watanni shida sannan za su ci gaba da fara tsakurar daunin da za su rika biyan bashin da su.
Wannan sahalewar karin wa’adin dai ta shafi har da wadanda aka bai wa lamuni na rukuni na biyu su 25 a cikin watan Afrilu.
Shugabar IMF ce Kristalina Georbina ce ta bayyana haka a ranar Litinin.
Ta ce wadanda ya kamata su fara biya daga 14 Ga Afrilu zuwa 18 Ga Oktoba, 2020 karin wa’adin ya shafe su.
Sai kuma rukuni na biyu wadanda za su fara biyan na su lamunin daga 14 Ga Oktoba, 2020 zuwa 13 Ga Afrilu, 2021.
Kasashen 28 sun hada da Afghanistan, Jamhuriyar Benin, Burundi, Burkina Faso, Afrika ta Tsakiya da kuma Chadi.
Akwai kuma Comoros Island, Congo, Djibouti, Ethiopia, Gambia da Guinea.
Sauran cikon kasashen su ne Guinea-Bissau, Haiti, Liberia, Madagascar, Malawi, Mozambique, Sao Tome da Principe, Sierra Leone, Solomon Island, Taiikistan, Tanzania, Togo da Yemen.