Ban yi wa masu zanga-zangar #EndSARS lakabi da marasa Addini ba kamar yadda Sahara reporters ta ruwaito – Zaharaddeen Sani

0

Fitaccen jarumin Kannywood ya karyata rahoton jaridar SAHARA REPORTERS wanda ta ruwaito wai jarumin ya yi kira ga matasan Arewa su far wa Aisha Yesufu sannan kuma wai ya kira masu Zanga-zangar #EndSARS marasa addini.

” Wannan jarida ta shirga karya ne kuma bata fadi gaskiyar abinda na ce ba.

” Idan ba su da wanda zai fassara musu abinda na ce da turanci ne, to bai kamata suyi gaban kan su ba wajen canja kalamai na don wata manufa tasu. Lallai na fadi kuma zan kara fadi Aisha Yesufu ta fito karara tana cewa wai matasan Arewa su fito su yi zanga-zanga, dukko mutumin da zai yi haka ba mutumin kirki bane, kuma zanga-zangar #EndSARS ba da manufar arziki suka fito da ita ba, dama akwai boyayyaiya kuma gashi yanzu ya fito fili, an ga abubuwan da ke faruwa a fadin kasar nan.

” Wannan kira da ta yi bai haifar da da mai ido ba, gashi an samu ɓarkewar ta’addanci yanzu a wasu wuraren.

A Bidiyon da Zaharadden yayi ya ce wannan talla da Aisha Yesufu ta rika yi na kira ga matasan Arewa su fito su yi zanga-zanga, suyi wa shugabannin su bore sam bai kamata ba, kuma duk abinda ya faru yanzu tana da hannu a ciki domin itace ta ingiza matasa har suka samu karfin aikata abunda ya ke faruwa.

” Ita kuma sahara reporters da ta ke karan farautar makiya Najeriya, su sani ba haka aikin jarida yake ba.

Jarumin yace yana nan akan bakar ta kuma bai janye koda kalma daya bace da yayi a bidiyonsa na farko sai dai idan za a yi masa fassara a fadi abin fa aka ce ba karya ba don son rai.

Share.

game da Author