Babu yarjejeniyar da Zamfara ta yi da Babban Bankin Najeriya CBN kan cinikin Gwal – Gwamnatin Zamfara

0

Kakakin gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, Zailani Bappa, ya karyata zargin wani lauya mai suna Joseph Silas, da ya ce wai Babban Bankin Najeriya, CBN, ta saka hannu a wata yarjejeniya da gwamnatin Zamfara domin kasuwancin Gwal da ake hakowa a jihar.

Bappa ya ce wannan Lauya bai yi amfani da sanin sa wajen fadin irin maganganun da ya yi.

Idan ba a manta ba, Lauya Silas ya yi korafin cewa CBN ta shiga yarjejeniyar ne duk da kuwa arzikin kasa mallakin gwamnatin tarayya ne ba ta jihar ba.

Sai da kuma a martanin Bappa ga Silas, ya ce jihar Zamfara bata taba hako gwal ta siyar ba.

” Arzikin kasa mallakin gwamnatin Tarayya ne, mu kan mu a jiahr Zamfara, muna siyan sa ne daga kamfanonin da gwamnatin tarayya ta amince da su rika hako gwal da sauran ma’adinai dake jibge a karkashin kasa a jihar.

Sabo da haka mutane irin su Silas da ke yin katsalandan a abubuwan da basu sani ba su shiga taitayin su tunda wuri, su rika yin bincike kafin su fito kafafen yada labarai suna babatu.

Idan ba a manta ba, gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, ya garzaya fadar shugaban kasa a makonni da suka gabata inda ya nuna masa wasu daga cikin gwal din da aka hako a jihar da kuma shirin da gwamnati ke yi na cin gajiyar wannan arziki da Allah ya ajiye a karkashin kasa a jihar.

Share.

game da Author