Kakakin Majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila, ya bayyana cewa ba zai sa hannun amincewa da Kasafin 2021 da ke gaban Majalisa ba, har sai an saka kuɗaɗen diyyar rayukan wadanda ƴan sanda su ka kashe tukunna.
Ya ƙara da cewa kuma tilas sai an saka kudaden bukatun Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU), sannan zai za hannu a kasafin.
Gbajabiamila ya yi wannan ikirari ne a lokacin da ya ke jawabi ga mambobin zauren Majalisar Tarayya a ranar Talata.
Wannan bayani ya zo daidai lokacin da zanga-zangar #EndSAR ta fara muni, har ta kai ga an kafa dokar-ta-baci a Lagos da Edo.
Gwamnatin Tarayya ta amsa cewa za ta biya dukkan bukatun masu zanga-zangar biyar. Sai dai kuma abin ya koma tarzoma, ganin yadda batagari su ka kwace ragamar zanga-zangar su ke kona dukiyoyi da kai wa jama’a da masu zanga-zanga hari.
Zuwa ranar Litinin, ‘yan sanda sun kashe masu zanga-zanga 12
Tun farko aks fara amsa bukatar su inda aka rusa SARS, sannan kuma Gwamnonin Jihohi sun kafa Kwamitin Binciken Wadanda SARS su ka kashe ko su ka danne wa hakki.
Gbajabiamila ya yi kira ga masu zanga-zanga su daina haka nan, “domin iyar wadda su ka kadai ta zama tahirin da zai sauya wata alkiblar kasar nan, ta hanyar saisaita wasu lamurran da ke tafiya ba daidai ba.”
“Ya kamata ku daina haka nan, domin batagari za su iya kwace ragamar zanga-zangar, su yi amfani da wannan dama su hargitsa kasar nan. Ko kuma su kara haifar da matsaloli a kan dimbin matsalolin da su ka dabaibaye kasar.”
Ya ce za su bi gida-gida su yi wa iyalan wadanda ‘yan sanda su ka kashe jaje. Kuma za a biya su diyya.
Discussion about this post