Jam’iyyar APC daga yanzu za ta rika tabbatar da cewa an daina cin nasara, amma wasu mambobi masu biyyaya ko ganimar kuturun bawa ba su samu ba.
Kan haka ne jam’iyyar ta ce za a rika tabbatar da cewa ana raba mukaman gwamnati da sauran mukaman hukumomi ana bai wa mambonim da aka tabbatar sun yi biyayya sau da kafa, ba tare da an manta da su ba.
APC ta ce Shugaban Riko na Jam’iyya, Gwamna Mai Mala-Buni na tuntubar Shugaba Muhammadu Buhari domin tabbatar da cewa an shigar da mambobin jam’iyya cikin mukaman siyasa.
Haka dai wata sanarwar da Jam’iyyar APC ta fitar ta nuna.
A taron manyan jam’iyya, an jinjina wa shugabannin APC wadanda su ka watannin baya.
Wadanda su ka saukan dai su ne wadanda su ka shude a karkashin shuhabancin tsohon shugaban APC, Adams Oshiomhole, wanda ya jefa APC cikin markabun rikicon da ta rika asarar jihohi, kamar an yi mata sammu.
Tun farkon hawan Shugaba Buhari APC ta rika zaizayewa, saboda dalilai da dama. Daga ciki akwai zargin nuna bangaranci ko kabilanci wajen nade-naden mukaman siyasa da na gwamnati a cikin hukumomi.
Akwai kuma zargin yin watsi da wadanda su ka fi yi wa jam’iyya hidima da kudaden su da jikin su kuma da lokutan su.
An yi ta korafe-korafen cewa manyan masu madafun gwamnati na watsi da ‘yan jam’iyya, su na bada sunayen abokai da dangin su ana ba su mukaman gwamnati da na siyasa.
Wasu sassan yankunan kasar nan ma na kukan cewa nade-naden da Buhari ke yi, ya na nuna fifiko a wani bangare ko yanki bisa ha sauran yankunan kasar.