An yi garkuwar da ma’aikacin lafiya a hanyar Kano

0

Masu garkuwar da mutanen sun yi garkuwa da wani ma’aikacin asibitin Dutse (FUD) dake jihar Jigawa a hanyar jihar Kano.

Kakakin asibitin Abdullahi Bello, ya sanar da hakada yake tattaunawa da manema labarai ranar Juma’a.

Bello ya ce masu garkuwa da mutanen sun arce da Shehu Abdulhamid dake tafiya tare da abokinsa bayan sun kamo hanyar zuwa jihar Jigawa daga Kano.

” Maharan sun tafi da Abdulhamid sun bar abokin a cikin mota a hanyar Kano zuwa Maiduguri a karamar hukumar Gaya.

” Masu garkuwan sun saki abokin domin ya sanar wa iyalen Abdulhamid abin da ya faru.

Bello ya ce tun farko dai maharan sun bukaci a basu naira miliyan 20 kudin fansan Abdulhamid amma daga baya suka rage zuwa miliyan 1.5 bayan an yi ta rokon su.

Bello ya ce sun sanar wa rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa abinda ya ya faru.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa Audu Jinjiri, ya tabbatar da abin da ya faru sai dai ya ce bincike ya nuna cewa an yi garkuwa da Abdulhamid tun a Kano ne kafin ya kamo hanyar Dutse.

A dalilin haka rundunar ta sanar wa rundunar ‘yan sandan jihar Kano domin daukan mataki.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano Abdullahi Haruna bai ce komai ba saboda ya ce bashi da cikakken bayani game da abin da ya faru.

Share.

game da Author