Kakakin asibitin Dutse (FUD) dake jihar Jigawa Abdullahi Bello ya bayyana cewa an sako ma’aikacin lafiyar asibitin da aka yi garkuwa da shi a hanyar Kano.
Bello ya ce an sako Shehu Abdulhamid bayan an biya kudin fansar sa, sai dai bai fadi ko nawa aka biya kudin fansan ba.
Idan ba a manta ba a ranar Litini din ta gabata ne masu garkuwar da mutanen suka yi garkuwa da Shehu Abdulhamid, wanda ma’aikacin asibitin Dutse (FUD) ne dake jihar Jigawa a hanyar jihar Kano.
An arce da Shehu Abdulhamid dake tafiya tare da abokinsa bayan sun kamo hanyar zuwa jihar Jigawa daga Kano.
Kakakin asibitin Abdullahi Bello, wanda ya sanar da haka ranar Juma’a ya ce bayan haka maharan sun bukaci a basu naira miliyan 20 kudin fansan Abdulhamid amma daga baya suka rage zuwa miliyan 1.5 bayan an yi ta rokon su.
Discussion about this post