An saka dokar Tabaci a jihar Filato, a karo na biyu

0

Gwamnan jiha Filato ya ce gwamnati ta saka dokar hana walwala a jihar Filato na awa 24, bayan wasu ‘yan Iska sun dirawwa inda aka ajiye kayan tallafin da jihar ta amshi rabonta ranar Larabar da ta gabata.

Dama kuma a yau ne gwamnatin jihar ta sassauta dokar hana walwala na awa 24 da ta saka ranar Laraba.

A ranar Asabar wasu ‘yan iskan gari sun ja zugar mutane suka far wa inda aka ajiye kayan tallafi da jihar ta amshi kason ta daga gwamnatin tarayya ranar Laraba domin raba wa mutane.

‘Yan iskan sun rika cewa kowa ya shiga ya kwashi rabon sa a koma gida.

Gwamna Lalong ya ce ya ba jami’an tsaro damar tabbatar da kowa ya bi dokar da ka saka ranar Asabar.

Share.

game da Author