An gurfanar da matar da ta gaggaura wa Ɗan sanda mari a Kotu

0

A ranar Litini ne babban kotun dake Zuba a Abuja ta gurfanar da wata mata mai suna Ene Ayuba kan laifin gaggaura wa Ɗan sandan mari a cikin caji ofis.

Kotu ta kama Ene mai shekaru 32 da laifuka biyu da suka hada da nuna wa jami’in tsaro fin karfi da cin mutuncin sa ta hanyar gaura masa mari a lokacin da yake bakin aikin sa.

Lauyan da ya shigar da karar Chinedu Ogada, ya bayyana a kotu cewa Ene ta ci zarafin Ɗan sandan ne ranar 4 ga watan Oktoba lokacin da jami’an tsaro ke yin bincike kan karan cin zarafin mijin Ene Ayuba da aka yi.

Ogada ya ce ana cikin yin wannan bincike ne sai Ene ta mike tsaye ta ko juya ta fuskanci wani Ɗan sanda mai suna Gwatana Friday, sai ko ta daga hannu ta shararar masa mari a cikin ofishin ƴan sandan dake Zuba.

Ya ce Ene ta mari Friday a gaban mai gidan hayan da suke a ciki, Aminu Maji, da wani mai suna Joseph Samuel da wasu mutane dake wurin.

Sai dai kuma Ene ta musanta wannan laifi a kotu.

Alkalin kotun Alhaji Gambo Garba ya bada belin Ene a kan Naira 500,000.

Ene za ta kuma gabatar da shaida na wani ma’aikacin gwamnati da ya kai mataki GL 10 kuma mazaunin kusa da kotun.

Za a ci gaba da shari’a ranar 9 ga watan Nuwamba.

Share.

game da Author