Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Gaba da Sakandare (NECO), ta bayyana cewa ta dage ranar fara Jarabawar Computer Studies Practical’ daga yau Litinin zuwa 16 Ga Nuwamba.
A ranar Litinin din nan ce aka tsara za a fara Jarabawar NECO din, amma an matsa da ita zuwa ranar 17 Ga Nuwamba.
Kakakin Hukumar NECO Azeez Sani, ya ce an matsa da NECO saboda zanga-zangar nuna fushi da jami’an SARS da ta buwayi manyan garuruwan kasar nan, musamman Lagos da Abuja.
Ya ce zanga-zangar wadda ta takaita zirga-zirgar motoci ta kawo tsaiko da cikas wajen raba kayan jarabawa a fadin kasar nan.
“Zanga-zangar #EndSARS da ta zo ba tare da masaniyar hakan na iya faruwa a lokacin fara jarabawa ba, ta kawo tsaiko da cikas din zirga-zirgar motoci bayan sun datse daidai ‘City Gate’ a Benin.”
Ya ci gaba da bayyana yadda aka datse hanya aka hana motocin da ke dauke da kayan jarabawa matsawa gaba ko baya.
“Amma dai mu na tabbatar maku cewa dukkanin kayan an samu dawo da su, Kuma Babu wanda ya salwanta ko ya lalace.”
Ana ci gaba da zanga-zangar #EndSARS a Lagos, Abuja, Anambra da sauran manyan garuruwan kasar nan.
A ranar Lahadi masu zanga-zanga a Abuja suka yi dafifi, dandazo da cincirindo a wajen harabar Babban Bankin Najeriya, CBN.
Sun kuma kwana a wurin zuwa wayewar garin yau Litinin. Sun kuma rika yin yekuwar cewa ba za su bari a bude CBN a yau Litinin ba.