An cafke ɗan sandan da ya bindige budurwarsa

0

Wani Ɗan sanda a jihar Legas sajen Eze Aiwansone ya dirka wa budurwarsa Joy Eze harsashi a fuska, ya shiga ta dama ya fito ta hagu.

Aiwansone ya aikata wannan ta’asa ranar 8 ga Oktoba a dalilin bayan sabani da ya auku a tsakaninnsu a lokacin da suke hira.

Cikin fushi Aiwansone ya jawo bindigar sa da ke makale a hammatar sa ya yako fuskance ta ya dirka mata, shi kuma Aiwansone ya arce.

Sai dai a ranar Alhamis kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Legas Olumuyiwa Adejobi ya ce sun kama Aiwansone.

Ya ce ɗan uwan Aiwansone da shima sufeton ƴan sanda ne, ya taso keyar Aiwansone ya danka wa jami’an tsaro.

Kwamishinan ƴan sanda Hakeem Odumosu ya yayi kira ga ƴan sanda da su rika maida hankali a wajen aikin su ba wurin da bai dace.

A watan Yuni PREMIUMTIMES ta bada labarin yadda rundunar ƴan sandan jihar Legas ta gano gawar wani saurayi da budurwarsa a wani gida dake Ilasan, a jihar.

Binciken da suka yi bayan gano wannan gawarwaki ya nuna cewa gawar namijin dai sunan sa Olamide Alli mai shekaru 25, da Chris Ndukwe, mai shekaru 39 a wannan gida da aka gano gidan marigayi Olamide Alli ne.

Kakakin rundunar Bala Elkana ya Sanar da haka yana mai cewa sun iske Chris kwance male-male cikin jini shi kuma Ali kumfar mutuwa a bakin sa.

“Akwai yiwuwar cewa Alli ne ya kashe budurwarsa Chris da wuka sannan shi kuma kwalkwali ruwan guba ya kashe kansa.

Share.

game da Author