An ɗaure wani sojan Najeriya shekaru biyar a gidan kurkuku, bayan samun sa da aka yi da laifin yi wa karamar yarinya fyaɗe.
Sojan mai suna Aliyu Yakubu, ya na da mukamin kofur, kuma kafin a yanke masa hukuncin daurin, sai da aka kore shi daga aikin sojan tukunna.
Kotun hukunta sojoji ta Runduna ta 7 ce ta yi wa Kofur Aliyu hukunci, inda aka tuhume shi da laifin keta haddin karamar yarinya mai shekaru 13 a Bama, Jihar Barno.
Mai gabatar da kara ya ce Yakubu ya ja karamar yarinyar zuwa cikin wani kangon gini, inda ya lakada mata duka, daga nan kuma ya yi mata fyade.
Mai gabatar da kara ya ce lamarin ya faru a ranar 1 Ga Yuli, 2018.
Kankanuwar yarinyar ta shaida wa kotu cewa sojan ya tare ta, sannan ya yi mata fyade a lokacin da ta bar gidan yayar ta, kan hanyar ta ta zuwa gidan mahaifiyar ta.
Sojan da ya gan ta, ya rika bin ta a baya, har sai da ya faki idon mutane, ya ja ta zuwa cikin kango, ya yi lalata da ita, bayan ya lakada mata duka.
“Ya fito da wuka ya yi barazanar kashe ta, idan har ba ta amince ya yi lalata da ita ba.
“Bayan ya yi mata tsirara, kuma ya ga ya kasa shigar ta, sai ya tambaye ta ko ta taba yin lalata. Yarinyar ta ce a’a. Daga nan sai ya shiga da karfin tsiya.
“Bayan ya gama yin lalata da ita, sai ya dauki bulo ya kwantsama mata a kai, ya bar ta cikin kangon a some.” Inji Mairuwa.
Bayan an kai yarinya asibiti, ta farfado, kuma da bincike ya taso ta iya shaida sojan da ya yi mata fyaden.
Sai dai sojan ya musanta, ya ce shi a ranar da abin ya faru ma ya na Maiduguri, ba shi da lafiya.
Amma kuma shaidu a cikin mambobin kotun sun same shi da laifi dumu-dumu.
Da ya ke yanke masa hukunci, Shugaban Kotu Burgediya ArikpoEkubi, ya ce an samu sojan da laifi biyu da ake tuhumar sa.
“Wannan kotu mai daraja ta same ka kai Aliyu Yakubu da laifin lalata da karamar yarinya da karfin tsiya, kuma ka azabtar da ita ta hanyar duka.
“Wannan kuwa ya saba wa Dokar Ka’idar Aikin Soja ta 78 da ta 104 da ke cikin Karamin Sashe na 2A.
“Ka ci amanar aikin soja da Rundunar Sojojin Najeriya ta damka maka. An ba ka amanar mutunta ‘yan Najeriya da kuma kare su, amma ka ci wannan amana.”
Kotun ta ce ta saurari rokon da sojan ya yi cewa wannan ne karo na farko da ya taba yin fyade, sannan kuma ya dade ya na aikin soja. Kuma ga shi ya na da iyali. Dalili kenan ta sassauta masa.
A kan haka ne aka yanke masa hukunci kamar haka:
“Tuhuma ta farko, daurin shekaru biyar. Tuhuma ta biyu kuma kora daga aikin soja.”
Kotu ta bada shawarar a maida yarinyar Lagos wajen wasu dangin ta, domin gudun tsangwamar jama’a.
Amma kuma kotun ta gano cewa an rigaya an yi wa yarinyar aure cikin wannan shekara, a cikin watan Maris, 2020.